Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Arne Slot, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yin isa wajen ganin sun sake lashe gasar firimiya ta kakar wasa mai zuwa wato kakar wasa ta 2025 zuwa 2026 domin dorawa daga nasarar da suka samu ta lashe gasar firimiya ta bana.
Slot ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya jagoranci kungiyar Liberpool ta lashe Premier League na 2024 zuwa 2025 na 20 jimilla, bayan da ta caskara kungiyar kwallon kafa ta Tottenham 5-1 ranar Lahadi a filin wasa na Anfield.
- Liverpool Sun Zama Zakaran Gasar Premier Bayan Lallasa Tottenham
- Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu
Tottenham ce ta fara cin kwallo ta hannun Dominic Solanke minti 12 da fara wasa, sai dai minti hudu tsakani Liberpool ta farke ta hannun Luis Diaz, sannan Mac Allister ya kara ta biyu.
Daf da za su je hutu ne kuma sai kungiyar ta Liberpool ta kara kwallo ta uku ta hannun Cody Gakpo, sai Mohamed Salah ya kara ta hudu, sannan Tottenham ta ci gida ta hannun Destiny Udogie. Kenan Liverpool ta samu damar daukar kofin Premier League na bana na 20 jimilla, iri daya da yawan na Manchester United. Liverpool ta samu damar lashe kofin bana, saura wasa hudu-hudu a karkare gasar ta bana, bayan da Arsenal ta tashi 2-2 da Crystal Palace ranar Laraba a filin wasa na Emirates kuma Liberpool ta dauki Premier na bana da maki 82, bayan cin wasanni 25 da canjaras bakwai aka doke ta wasa biyu. Arsenal ce ta biyun teburi mai maki 67, bayan cin wasa 18 da canjaras 13 da rashin nasara uku a babbar gasar ta Ingila.
Liverpool ta yi wannan kwazon karkashin sabon koci, Arne Slot da ta dauka kan a fara kakar nan, wanda ya maye gurbin Jurgen Klopp, wanda ya yi ritaya. Tun farko Liberpool ta yi fatan lashe kofi hudu a kakar nan, sai dai an yi waje da ita a League da FA Cup. Haka kuma ta yi ban kwana da Kofin Zakarun Turai na kakar nan, bayan da Paris St Germain ta yi waje da ita a zagaye na biyu.
Tuni dai an samu gurbi ukun da suka yi ban kwana da Premier League da za su koma buga Championship a badi da suka hada da Ipswich da Leicester da kuma Southampton.
Yanzu inda ake tata-burza shi ne gurbin da za su wakilci Ingila a badi a gasar zakarun Turai. Kungiya biyar ce za ta wakilci Ingila a badi a Kofin Zakarun Turai, yayin da watakila su zama shida da zarar Manchester United ko Tottenham daya a cikinsu ta lashe Europa League. Manchester United da Tottenham duk sun kai zagayen daf da karshe a Europa League.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp