Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti mai mutum 18 domin sa ido da bin diddigin yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya), ke gudanar da mulki tun bayan ayyanar dokar ta-ɓaci a jihar.
Shugaban. Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce kafa kwamitin zai taimaka wajen tabbatar da shugabanci na gaskiya da kuma ganin an bi doka yadda ya kamata a jihar.
- EFCC Ta Kama Matashi A Kaduna Bisa Zargin Wulaƙanta Naira A Bidiyon Barkwanci
- Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
Ya ce, “Wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da bin doka a Jihar Ribas, ba tare da wata ɓoyayyar manufa ba.”
Kwamitin, wanda shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele ke jagoranta, ya ƙunshi Sanata Adamu Aliero, Osita Izunaso, Osita Ngwu, Kaka Shehu, Aminu Abass, Tokunbo Abiru, da Adeniyi Adebire, tare da wasu ƙarin mambobi.
Tun a watan Maris ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP, da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, wanda yanzu ke cikin gwamnati a matakin tarayya a matsayin minista.
Rikicin ya janyo zaman ɗari-ɗari a jihar, lamarin da ya sa shugaban ƙasa ya tsoma baki domin kare zaman lafiya da doka a jihar.
Gwamnan riƙo Ibok Ete Ibas ne aka ɗora don tafiyar da mulki har sai an samu daidaito a siyasar jihar.
Ana sa ran kwamitin za ta kai rahoto a duk matakin da take gani ya kamata a ɗauka domin kare mulkin dimokuraɗiyya da kwanciyar hankali a Jihar Ribas, wadda ke daga cikin muhimman jahohin da ke da tasiri a tattalin arziƙin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp