Hausawa na cewa, makashin maza, maza ke kashe shi watarana, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tabbatar da gaskiyar wannan karin magana a filin wasa na Parc Des Prince da ke birnin Paris na kasar Faransa a wasan na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai, UEFA.
Arsenal ta ziyarci PSG domin buga wasan na kusa da na karshe na Gasar UEFA bayan ta sha kashi a gidanta a wasan farko da suka buga a watan jiya, a wasan yau kuma Paris din ce ta kuma doke Arsenal da ci 2-1 wanda ya zamo 3-1 jimilla.
- Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?
- An Tabbatar Da Ficewar Sanata Sumaila Daga NNPP Zuwa APC A Majalisa
Kwallayen da Fabian Ruiz da Achraf Hakimi suka ci ne ya janyo wa PSG nasarar tsallakawa zuwa wasan karshe na gasar a karo na biyu a tarihinta, za ta hadu da Inter Milan wadda ta fitar da Barcelona ranar 31 ga watan Mayu na wannan shekarar.
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp