Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi gargaɗin cewa Isra’ila za ta ɗauki irin matakan da ta ɗauka kan Hamas a Gaza a kan Iran, bayan hare-haren da ‘yan tawayen Houthis da ke samun goyon bayan Iran suka kai wa filin jirgin sama na Ben Gurion.
“Na yi gargaɗi Shugabannin Iran da ke ba da kuɗi da makamai ga ƙungiyar ƴan ta’adda ta Houthis a cikin wata sanarwa. “Kuna da alhaki kai tsaye. Abin da muka yi wa Hezbollah a Beirut, Hamas a Gaza, da (tsohon shugaban Syria Bashar) Assad a Damascus, za mu yi muku a Tehran.”
- Mene Ne Shirin Nukiliya Na Iran Kuma Me Amurka Ke So Ta Yi?
- Hamas Za Ta Saki Dukkan Fursunonin Isra’ila Da Ke Hannunta
Ƴan tawayen Houthis na Yemen, tare da Hezbollah da Hamas, wani ɓangare ne na hanyar kai hari na Iran a kan Isra’ila da ƙawarta, Amurka.
Hezbollah ta fara kai hare-hare a watan Oktoba 2023 don tallafawa Hamas, bayan kai harin da ba a taɓa ganin irinsa ba a kudancin Isra’ila.
A cikin shekarar da ta ƙare da yarjejeniyar sasantawa a watan Nuwamba, Sojojin Isra’ila sun kai wa Hezbollah hari, yayin da shugabannin Hamas suka yi asarar rayuka da yawa a yakin da aka fara a ranar 7 ga Oktoba.
Houthis sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra’ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙi da ‘yan tawayen ke yi kan Isra’ila, a matsayin tallafin ga Falasdinawa a Gaza. Iran ta musanta cewa ta goyi bayan Houthis a harin.
Duk da haka, Isra’ila ta mayar da martani kan Houthis tare da kai hare-hare kan filin jirgin sama na babban birnin Sana’a da ke hannun ‘yan tawayen da kuma tashoshin wutar lantarki a kewayen birnin.
Amurka da Houthis sun cimma yarjejeniyar sasantawa, kamar yadda Oman ta sanar a ranar Talata, inda ta ce yarjejeniyar za ta tabbatar da ” ‘yancin kewayawa” a cikin bahar maliya, inda ‘yan tawayen suke kai hare-hare kan jiragen ruwa.
Houthis sun yi alƙawarin ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila da jiragen ruwan Isra’ila a cikin bahar Maliya duk da yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen hare-haren da Amurka ta kai wa Yemen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp