Biyo bayan kokarin da ake yi na sake farfado da babban wajen da Jiragen Ruwa ke tsayawa wato OMT da ke a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne, Babban Jami’i da ke lura da OMT Jim Stewart, ya jinjinawa Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Qasa NPA Dakta Abubakar Dantsoho.
Stewart, ya yabawa Dantsoho ne, kan goyon bayan da yake ci gaba da bayar wa da kuma kara inganta ayyukan Hukumar, inda ya ce, NPA a karkashin shugabancin Dantsoho, ya samar da dibin ci gaba ga ci gaban, musamman babban wajen da Jiragen Ruwa ke tsayawa na Tashoshin Jiragen Ruwan Qasar.
- Shugaban NPA Dantsoho Ya Bayyana Aniyar Inganta Ayyukan Hukumar A Wannan Shekarar
- Hukumar NPA Ta Ce Za A Kammala Aikin NSWP A Zango Na Daya A 2026
A cewarsa, Shugaban ya samar da wannan nasarar ce a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne, a ranar 16 na watan Afirilun 2025 wanda hakan ya nuna karin samun ci gaba da na wajen wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci, a Afirka ta Yamma.
Ya kara da cewa, isowar Jirgin Ruwa na daya daga cikin manyan Kafanonin Jiragen Ruwa da ke yin jigilar kaya da ke a yankin Asia ga babban wajen da Jiragen Ruwa ke tsayawa a OMT, hakan ya kara nuna sake farfadowar babban wajen tsayawar Jiragen.
Jirgin Ruwan Kamfanin ya iso Tashar ta Onne ne, dauke da Kwantainoni1, 250, inda kuma ya aka loda masa wasu Kwantainoni 1,619
A jawabinsa a wajen tarbar Jirgin Ruwan na na yankin Asia Jim Stewart, ya bayyana jin dadinsa ga Hukumar ta NPA, bisa goyon bayan da ta bayar wajen samar da kyakyawan yanayi a babban wajen da Jiragen Runwan na Tashar Onne suke tsayawa.
“Muna da kyakaywar dangantakar gudanar da ayyuka da Manajan Tashar ta Onne Mista Abdulrahmon Hussain da kuma sauran ‘yan tawagar Hukumar ta NPA, “Inji Stewart.
Ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancin shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho, wanda kuma kashin bayan duk wata nasara da muka zamu.
“Sake farfado da babban wajen tsayawar Jiragen Ruwan a Tashar Onne, hakan ya kara mana kwarin Guiwa”. A cewar Stewart.
Kazalika, Stewart ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara samar da wadatattun kudade domin a kara fadada aikin yasar Gulnin da ke a Tashar ta Onne.
Tashar ta Onne, musamman domin a samu karin yawan Jiragen Ruwa masu tsayawa a Tashar, wanda hakan zai kuma kara taimaka wa, wajen bunkasa hada-hadar kasuwanci a Tashar.
“Mun shirya tsaf, domin tarbar Jiragen Ruwa masu yawa da suka, amma domin mu ci gaba da cin gajiyar da ta kamata a Tashar ta Onne, akwai matukar bukatar a mayar da hankali wajen kara fadada yin haka a Gulbin da ke a Tashar, ” Inji Stewart.
“Mun kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara taimaka wa Hukumar ta NPA da kudaden da suka kamata, musamman domin a kara fadada hakar Gubin na Tashar Onne,” A cewar Stewart.
Ya bayyana cewa, biyo bayan isowar da Jirgin Ruwa na Kota Cempaka ya yi a Tashar ta Onne, a shekarar da ta gabata, wannan nasarar ta nuna irin yadda ake ci gaba da samar da dabarun zuba hannun jari a Tashar ta Onne da kuma yadda aka kara mayar da hankali, wajen kara inganta ayyukan na Tashar.
Kazalika, Stewart ya jaddda mahimmancin zamanantar da Tashar ta Onne, ta hanyar gyare-gyaren da ake yi a Tashar, matsayin wata manufa ta rage cunkoson Jiragen Ruwa da ke tsayawa Tashar.
Ya yi nuni da cewa, ganin yadda irin wadannan manyan Jiragen Ruwa suka fara isowa Tashar ta Onne, hakan kara taimaka wa, wajen kara bunka tattalin arziki ga Tashoshin Jiragen Ruwan kasar nan,
Ya kara da cewa, hakan zai kuma kara taimaka wa, wajen ragewa ‘yan kasuwar da ke shigoa da kayan zuwa cikin kasar nan da kuma rage cazarsu kudin harajin fitar da kaya zuwa ketare.
“Wannan nasarar bai wai kawai ta shafi Tashar ta Onne bane kadai, har da daukacin tattalin arzikin kasar nan, kuma sake farfadowar Tashar ta Onne, za ta kara bayar da wata damar kara shigowar Jiragen Ruwa cikin kasar nan, wanda hakan zai kuma kara samarwa da Nijeriya, da wasu kudaden shiga, “Inji Stewart,
Shi kuwa a na sa jawabin Hukumar ta NPA wani babban Direban Jirgin Ruwa a Tashar ta Onne Yakubu Ezra, ya jaddada cewa, Hukumar ta NPA, a shiraye take wajen karbar duk wasu Jiragen Ruwa da za su sauka a Tashar ta Onne.
“An tanadar da isassun kayan aiki na fasahar zamani Tashoshin Jiragen Ruwan kasar nan, musamman domin a Jiragen Ruwan su rinkaa tsakyawa a cikin sauki, tare da kuma bai wa ma’aikatan horon da ya dace, “ Inji Yakubu.
A cewasa, samun nasarar ta isowar Jirgin Ruwan na Kota Carum alamu ne da nuna irin karfin Tashar ta Onne da kuma irin kwarewar da Tashar take da shi.
Ganin yadda Jiragen Ruwa da dama daga Afrika ta Yamma ke shirin isowa Tashar ta Onne, hakan ya kara nuna irin ingantattun kayan aiki da damarun da aka samar a Tashar, wanda hakan zai kara bayar da dama wajen kara janyo zuwan Jirage da kasa da kasa, zuwa Tashar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp