Dakarun rundunar soji ta ‘Operation Hadin’ Kai sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi na yakar ‘yan ta’addan Boko Haram, bayan wani gagarumin farmaki da suka kai a dajin Sambisa.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kyaftin Reuben Kovangiya, mukaddashin mataimakin darakta na ofishin hulda da jama’a na rundunar soji ta Operation Hadin Kai, ya fitar ranar Litinin a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
- Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar
- Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma
A ranar Lahadi 11 ga watan Mayun 2025 ne dai aka kai farmakin a yankin Ladin Buttu, wanda aka fi sani da fitacciyar maboyar ‘yan Boko Haram, hakan ya yi sanadin kashe biyar daga cikin ‘yan ta’addan tare da raunata da dama bayan wani kazamin musayar wuta da suka yi.
Sojojin sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyar da sauran makaman yaki daga a yayin artabun.
Majiyoyin sojin sun bayyana cewa, farmakin wani sabon shiri ne na sake tarwatsa shirin ‘yan ta’addan da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su wajen kai muggan hare-hare a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp