Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya bayyana cewa yana da mafita ga matsalolin da yake fuskanta, kuma ya gargaɗi magoya bayansa da su daina aikata abubuwan da ke jefa shi cikin ƙarin matsaloli.
Fubara ya bayyana haka ne a yayin taron addu’o’i na tunawa da marigayi dattijo Edwin Clark a birnin Fatakwal ranar Lahadi.
- Nazarin CGTN: Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Latin Amurka Na Kara Samun Karbuwa Tsakanin Jama’a
- Ma’aikatar Kasuwanci: Sanarwar Da Sin Da Amurka Suka Fitar Muhimmin Mataki Ne Na Warware Sabaninsu
“Ka da ku yi abubuwa kawai saboda kuna so, ku yi abin da nake so. Ni nake cikin wannan hali, kuma na san hanyar da zan bi na fita daga ciki,” in ji Fubara.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ayyukan magoya bayansa na kawo masa cikas maimakon taimaka masa wajen samun zaman lafiya.
Tun da farko, Fubara ya ce ba shi da sha’awar komawa kujerar gwamna saboda “raina ba ta tare da kujerar tun tuni.”
Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida.
Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp