Ƴan majalisar tarayya guda biyu daga jihar Kano, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun sanar da barin jam’iyyar NNPP zuwa APC a yayin zaman majalisar ranar Alhamis, suna mai nuni da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar.
Shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar ficewarsu a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa Kabiru Rurum mai wakiltar mazaɓar Rano da Kibiya da Bunkure da Hon.Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Karaye da Rogo.
- Dole Kwankwaso Ya Nemi Afuwarmu Kafin Ya Komo APC
- Gwamna Yusuf Ya Yi Barazanar Ƙwace Lasisin Jerin Gidajen Kwankwasiyya, Amana Da Bandirawo
Ko da a kwanan baya ma Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da wasu sun fice daga jam’iyyar NNPP, su ma dai sun ce rikicin ne ya fitar da shi.
Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje da wasu manyan ƙososhin jam’iyyar sun halarci taron sauyin sheƙar a majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp