ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

JAMB Ta Ƙaddamar Da Binciken Gaggawa Kan Sakamakon Jarrabawar Bana Bayan Jerin Ƙorafe-Ƙorafe 

by Khalid Idris Doya
7 months ago
JAMB

Hukumar kula da shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta kaddamar da wani bita cikin gaggawa kan tsarin Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (UTME) na shekarar 2025, biyo bayan korafe-korafe da dalibai da iyaye ke yi a fadin kasar na tare da zargin rashin bin ka’ida da kuma sabani a sakamakon jarabawar.

Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan da hukumar ta sake sakamakon jarabawar bana, inda hukumar ta tabbatar da cewa ta samu jerin korafe-korafe da daman gaske. Dubban dalibai ne dai suka yi fatali da kin amincewa da sakamakon da suka samu a jarabawar, lamarin da ke janyo kokonto da shakku kan ingancin tsarin da ake bi.

  • JAMB Ta Dakatar Da Wasu Jami’anta Saboda Tilastawa Wata Daliba Cire Hijabi
  • Gwamnatin Kano Ta Soke Tsaftar Muhalli A Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB

Dalibai da dama sun shiga shafukan sada zumunta, suna zargin hukumar JAMB da gazawa ta bangaren samun tangardar na’ura da suka yi imanin cewa ya yi illa ga kwazonsu da kokarinsu a yayin jarabawar.

ADVERTISEMENT

Da yake magana a Abuja, mai magana da yawun hukumar JAMB, Dakta Fabian Benjamin ya tabbatar da cewa hukumar tana duba na’urorinta a kai a kai gabanin ma gudanar da jarabawar.

“Muna hanzarta sake duba jarabawarmu na yau da kullun, wanda zai bincika kowane bangare na tsarin UTME, tun daga rajista zuwa jarrabawa da fitar da sakamako,” in ji Benjamin.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

Ya yi nuni da cewa hukumar tana aiki ne tare da hadin gwiwar abokan huldar waje, da suka hada da kungiyar kwararrun na’urar kwamfuta ta Nijeriya, da manyan masu jarrabawa daga manyan makarantu, da kungiyar ilimi da cibiyar bincike a Afirka. Wadannan hadin gwiwar, in ji shi, suna da nufin samar da ingantaccen bincike da kuma sahihin bincike.

“Idan an gano cewa an samu tangarda a na’ura, to za a dauki matakan gyarawa ba tare da bata wani lokaci ba,” Benjamin ya tabbatar.

Duk da wannan tabbacin da aka bayar, sama da dalibai 8,000 ne suka shigar da korafinsu a hukumance suna cewa an samu matsaloli na na’ura sosai a yayin jarabawa. Abubuwan da aka ruwaito sun hada da daskararrun allon kwamfuta, jinkirin shiga cikin tsarin zana jarabawar daga ita kwanfutar, da karewar zaman jarrabawa ba zato ba tsammani.

Binciken farko na sakamakon UTME na 2025 ya nuna cewa sama da kashi 78 na sama da dalibai miliyan 1.9 sun samu maki kasa da 200 cikin matsakaicin maki 400. Alkaluman sun kara zurfafa shakku na gazawar fasaha ko na tsari.

Benjamin ya ce duk da haka, lamarin ya tsaya kan sakamakon kamar yadda aka fitar a halin yanzu, yana mai bayyana cewa sun yi daidai da hakikanin kwazon da dalibai suka nuna. Har ila yau, ya amince da alhakin hukumar ta binciki duk rahotannin da suka dace na abubuwan da suka faru.

Sai dai hukumar ta nemi a kwantar da hankali har zuwa lokacin da za ta kammala binciko shin an samu matsala a tsarin jarabawar ko kuma gazawar kwazon ɗalibai ne.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025
Ilimi

Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025

November 30, 2025
Next Post
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Kassara Kamfanonin Fasaha Da Na AI Na Sin

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Kassara Kamfanonin Fasaha Da Na AI Na Sin

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.