Kwalejin horon Malaman makaranta ko Katsina Kwalej ta Katsina ita ce tsohuwar makaranta a Arewacin Nijeriya wadda aka gina ta. a shekarar 1921 dalibai suka fara karatu a cikinta 1922.
An gina tane da tubulin kasa ne wanda aka kona.Halin da ake ciki yanzu ta zama wurin ziyara ind masu yawo shakatawa suke zuwa su kashe kwarkwatar ido duk lokacin da suka zo Katsina.An maida wurin inda ya kasance wurin tarihi ranar 23 ga Afrilu 1959 inda ake kiran wurin da suna Katsina Museum .Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa Firayim Ministan Nijeriya na farko da kuma Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato Firimiyan Arewa duk,sun halarci makarantar.
- Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina
- Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Kaba Aiki A Katsina
An gina Kwalejin ne a kofar sauri wadda take cikin birnin Katsina,kafin dai bayyanar ilimin zamani wanda ake kira da suna Boko,ilimin addiin musulunci a wancan lokacin shi ne ake amfani da shi ne ake amfani da shi.Wannan dalilin shi yasa Turawan mulkin mallaka a wancan lokacin suka fuskanci matsala gare su da suke niyyar shigo da ilimin zamani a lokacin,don haka sai suka bi lamarin,a hankali inda daga baya suka kafa makarantar Katsina Kwalej a shekarar 1922.
Hada Arewacin da Kudancin Nijeriya da aka yi a shekarar shi yasa bukatar ilimin zamani ta taso, bayan shekara ashirin da kasancewar su, ba lokacin bangaren Arewa musamman ma lardunan da suke karkashin ta basu da ‘yan asalin wurin wadanda suke da ilimin zamani sosai da har, za’a iya basu mukamin Akawu su yi aiki a ofisoshin gwamnati da kuma sassan. Gwamnan Arewa Sir Hugh Clifford,shi ya sa aka kafa Kwalejin domin horar da ‘yan Arewa wadanda za su yi aiki a makarantun Lardunan.
An taba jin Sir Clifford yana cewa lokacin da yake bude makarantar da aka sa ma suna Katsina Kwalej cewa babban dalilin kafa ita makarantar shi ne a koyawa Malamai wadanda, “su ma a matsayinsu na Malamai a gaba watarana sune za su iya kasancewa Shugabanni,wadanda ana sa ran halayensu na iya gyaruwa domin a daidaita al’umma.”Kwalejin Katsina ta fara ne da daukar dalibai 50 wadanda suke daga Lardunan Arewacin Nijeriya.
A wancan lokacin,Mrs. Bintu M.Sadik, cewa tayi Sir S.M. Banaman shi ne Shugaban Kwalejin na farko duk kuma Malaman Turawa, daga baya ne aka dauke Hausawa ‘yan asalin wurin saboda su koyar da Hausa da kuma al’amarin daya shafi addinin musulunci.Ta ce mshahuran ‘yan Arewa sun halarci Kwalejin daga cikinsu akwai Firayim Minista na farko Abubakar Tafawa Balewa,Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa, da kuma Sir Kashim Ibrahim, da dai sauran wasu duk sun halarci Kwalejin ta Katsina
An samu labarin kasar Katsina ta taba kasancewa wata babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara. Wannan shi tun lokacin da aka hade Arewa da Kudancin Nijeriya Katsina tana daya daga cikin wuraren da hanyar jirgin kasa ta bi ko kuma Layin Dogo a lokacin.Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shi ya bada wurin da aka gina Katsina Kwalejin ne a cikin gonarsa da ke Rafukka a lokacin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp