Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa an kammala jigilar maniyyata masu zuwa aikin hajji daga jihohi 12 na Nijeriya zuwa Saudiyya.
Jimillar maniyyatan da aka jigilarsu, sun kai mutum 25,702.
- Kasar Sin Na Adawa Da Kai Wa Fararen Hula Da Kayayyakin More Rayuwa Hari A Sudan
- Yankin Taiwan Ba Shi Da Iko Ko Hujjar Halartar Taron WHA
Jihohin da aka kwashe maniyyatan daga cikinsu sun haÉ—a da: Osun, Oyo, Adamawa, Filato, Ekiti, Imo, Legas, Abiya da Edo.
A cewar NAHCON, jirage 63 ne suka É—auki waÉ—annan maniyyata cikin kwana goma, kuma har yanzu ba a samu wata matsala ba tun lokacin da aka fara jigilar.
Hukumar ta ce a wannan shekarar, mutum 43,000 ne ake sa ran za su sauke farali a ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji.
Wani jami’in hukumar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa tsare-tsaren da hukumar ta É—auka sun taimaka sosai, inda komai ke tafiya cikin kwanciyar hankali a Saudiyya.
An fara jigilar maniyyatan ne a ranar 9 ga watan Mayu 2025 a filin jirgin sama na Owerri da ke Jihar Imo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp