Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya zargi wasu ‘yan siyasa da jami’an tsaro da taimaka wa ‘yan Boko Haram ta hanyar ba su bayanai da kuma haɗa kai da su.
Gwamnan ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central.
- Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5
“Akwai wasu daga cikin jami’an tsaro, ‘yan siyasa da ma wasu daga cikin al’umma da ke tsegunta sirri da taimaka wa Boko Haram. Dole ne a ƙarfafa tsaro kuma a hukunta masu irin wannan aiki ba tare da tausayi ba.”
Masana tsaro da dama, ciki har da Dakta Audu Bulama Bukarti, sun ce wannan zargi mai girma ne da ya kamata a ɗauke shi da muhimmanci.
Bukarti ya ce, “Idan gwamna irin Zulum ya faɗi haka, to akwai abin da ya sani. Wannan ba magana ce kawai ba. Dole a bincika sosai a gano gaskiya.”
Masana sun yi kira ga hukumomi da su yi bincike mai zurfi don gano waɗanda ke taimaka wa Boko Haram sannan a hukunta su domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp