Mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa ƴan ta’adda da masu aikata laifuka sama da 13,500 ka kashe su a duk faɗin Nijeriya tun lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.
A wani taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, Ribadu ya ce adadin ya nuna tasirin ayyukan Sojoji a yankunan da ake rikici. “Sojojinmu sun kashe ‘yan ta’adda 13,543. Mun kuma kwato ko lalata harsasai 252,596,” in ji shi.
Ribadu ya kuma bayyana cewa aƙalla mutane 124,408 – waɗanda suka haɗa da tsoffin mayaƙan Boko Haram da ISWAP da iyalansu – sun miƙa wuya ga hukumomin Nijeriya tun farkon gwamnatin Tinubu. “Waɗannan ba kawai sun miƙa wuya ba ne, suna cikin tsarin gyara ta hanyar shirinmu na kwantar da hankali da sake dawo da su cikin al’umma,” ya bayyana.
Mashawarcin tsaron ƙasar ya danganta nasarorin da ake samu wajen yaƙi da ta’addanci da cikakken haɗin gwuiwa tsakanin hukumomi, da ƙarin ƙaimi da aka saka wajen tattara bayanai, da kuma kwarin gwuiwar siyasar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC suka nuna.
“Mun samu ci gaba sosai,” in ji Ribadu. “Wannan ba ya faru ba ne. Sakamakon dabaru ne, da jagoranci mai himma, da sadaukarwar dakarun tsaronmu.” Taron ya kasance wani fata don gwamnati da shugabannin jam’iyyar su nuna nasarorin da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp