An kori shugaban jam’iyyar APC reshen Jihar Enugu Ugo Agbalah daga jam’iyyar.
An sanar da korar shugaban jam’iyyar a ranar Juma’a.
- Babu Wanda Zai Fice Daga NNPP Da Zai Girgiza Siyasar Kwankwaso – Kofa
- An Harbe ‘Yansanda Biyu Har Lahira A Shingen Bincike A Filato
Wasikar korar shugaban, Mista Aduma Ferdinand, da sakatare, Mista Onyia Francis, suka sanya wa hannu ga manema labarai a daren Juma’a a Enugu, ta bayyana cewa an dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar daga jam’iyyar ne saboda ya kasa gurfana a gaban Kwamitin amsa zarge-zargen da ake masa.
An tattaro cewa wani dan karamar hukumar ya rubuta takardar koke akan Agbalah, inda ya zarge shi da cewa ba shi da rajista a jam’iyyar a mazabarsa.
Sauran zarge-zargen sun hada da ruguza jam’iyyar, lamarin da suka ce zai iya sa ba za su iya lashe zabe a 2023 ba da kuma rashin halartar taron jam’iyyar a matakin mazaba da kuma rashin bada hadin kai.
LEADERSHIP ta tuna cewa Agbalah na da wasu kararraki da ke gaban kotu inda ake zarginsa cewa ba dan jam’iyyar APC bane.
Da aka tuntubi Agballah, ya yi watsi da korar tasa, inda ya ce wadanda suka yi yunkurin korar tasa mambobin bogi.
Ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Kwamared Kenneth Oforma, inda ya yi zargin cewa shugabannin jam’iyyar a jihar ba su da ikon aikata hakan.
“Mutumin da sa hannunsa yake a matsayin shugaba ba shi ne shugaban mazaba ba, shi ne shugaban Unguwan Chinedu Ezeago.