• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kashinku Ya Bushe: Sojoji Sun Lashi Takobin Kawo Ƙarshen ‘Yan Ta’adda A Zamfara Da Katsina 

by Sadiq
4 months ago
Sojoji

Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta gargaɗi ‘yan bindiga da suka addabi Zamfara, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma da su fice daga maɓoyarsu ko su fuskanci mummunan luguden wuta ta sama.

Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ne, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin gudanar da motsa jiki a Abuja.

  • An Kashe Wani, Wasu Sun Jikkata A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Neja
  • Hajjin Bana: Falalar Tsayuwar Arfa

Ya ce za su ci gaba da kai farmaki kan ‘yan ta’adda a Borno da sauran yankunan Arewa maso Gabas.

Ya ce dakarun sama ba za su zuba ido ba yayin da masu aikata laifi ke kawo ruɗani a cikin ƙasa.

“Ga maƙiyan Nijeriya, ku sani: ba za ku samu wajen ɓuya ba. Za mu same ku kuma mu kawar da ku,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan.

Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata.

A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka.

Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da cikakken lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa ba.

Don haka, ya amince a gina sababbin wuraren motsa jiki a sansanonin rundunar Sojin Sama da kuma siyan sabbin kayan motsa jiki don raba wa sassan rundunar sama da 22.

Ya bayyana cewa aikin motsa jikin ba wai motsa jiki kawai ba ne, amma yana nuna karfi da daidaito da kuma ƙudirin rundunar wajen kare Nijeriya.

Ya buƙaci dakarun su kasance masu jajircewa da haƙuri domin cimma zaman lafiya.

Wannan aikin motsa jiki ana yin sa ne sau uku a shekara a dukkanin sassan rundunar Sojin Sama domin ƙarfafa jiki, haɗin kai da kuma nuna wa jama’a da maƙiya cewa rundunar Sojin Sama ta kasance cikin shiri, kuma za ta ci gaba da kare Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Kotu
Manyan Labarai

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Next Post
Trump Ya Umarci A Bincika Lafiyar Ƙwaƙwalwar Tsohon Shugaban Ƙasa Biden Yayin Mulkinsa

Trump Ya Umarci A Bincika Lafiyar Ƙwaƙwalwar Tsohon Shugaban Ƙasa Biden Yayin Mulkinsa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

October 14, 2025
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

October 14, 2025
Kotu

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

October 14, 2025
Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

October 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.