• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Trump Ya Umarci A Bincika Lafiyar Ƙwaƙwalwar Tsohon Shugaban Ƙasa Biden Yayin Mulkinsa

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umurci a gudanar da bincike kan lafiyar ƙwaƙwalwar tsohon shugaban ƙasar Amurka Joe Biden lokacin da yake kan mulki, yana zargin hadiman sa da ƙulla wani “makirci” don yaudarar jama’a game da halin lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Trump ya mayar da hankali kan amfani da na’urar autopen, wadda ke saka hannu ta atomatik don amincewa da takardu – wata na’ura da shugabanni da dama, ciki har da Trump kansa, suka taɓa amfani da ita. Sai dai ya ce amfani da ita a lokacin Biden na iya zama shaida cewa ana ɓoye gaskiyar halin da tsohon shugaban ya shiga ciki.

  • Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan Crypto 
  • Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai

“Makircin nan na daga cikin mafi haɗari a tarihin siyasar Amurka,” inji Trump a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Joe Biden, mai shekaru 82, ya ƙaryata zargin, yana mai cewa da’awar Trump ba ta da tushe kuma siyasa ce kawai ke motsa shi. “Ni nake yanke hukunci lokacin mulkina,” inji Biden. “Dokoki, da yin afuwa, da dukkan umarnin shugabanci – ni nake yinsu.”

Sai dai Jam’iyyar Republican ta ƙara matsa lamba wajen tambayar ko Biden yana da lafiyar da ta dace domin yin mulki. Wani kwamitin Majalisar Wakilai da jam’iyyar ke jagoranta na neman wasu manyan jami’an gwamnatin Biden domin su ba da shaida game da yanayin lafiyar sa tun lokacin yana shugaban ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun da wuri, musamman ganin yadda aka ce ta bazu zuwa ƙasusuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga
Kasashen Ketare

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Sace 2 A Wurin Haƙar Ma’adanai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Sace 2 A Wurin Haƙar Ma’adanai

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Trump

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.