Shahararren mawakin siyasar nan na ƙasar Hausa kuma mawakin shugaba Buhari, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, ya gargaɗi shugaban ƙasa Buhari da kar ya sake ya yaki, Bola Ahmad Tinubu, saboda ya taimaki shi a lokacin da yake buƙatar taimako.
Rarara ya bayyana haka cikin wani faifon bidiyo da ya karade kafafen yada labarai na zamani dangane da batun da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ke cewa, Bola Ahmad Tinubu, ya yi wa shugaban ƙasa Buhari gorin taimako.
- 2023: Tinubu Ne Mafi Dacewa Da Zama Shugaban Kasa —’Yan Kudu Maso Yamma
- Babu wata Yarjejeniya Da Aka Gindaya Cewa Za A Ba Tinubu Shugaban Kasa Bayan Buhari -Yerima
Wannan magana da Bola ya yi da alama bata yi wa wasu daga cikin magoya bayan shugaba Buhari daɗi ba, saboda suna ganin babu wani dalili da zai sa, Bola Ahmad Tinubu, ya share wuri yana maganganu masu kama da suka ta kai -tsaye ga shugaba Buhari.
Inda har suke ganin kamar Bola Ahmad Tinubu yana ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa, saboda neman mulki har yana ƙoƙarin cin fuskar shugaban ƙasa Muhammad Buhari.
Mawakin wanda ya ce Bola Ahmad Tinubu ya taimaki shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, kuma ko shi Buhari ba zai ƙaryata hakan ba, ya ce har na kusa da Buharin ma sun san haka.
An ruwaito shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu yana cewa za su iya ɗaukar mataki akan Bola Tinubu dangane da wadancan kalamai na shi.
Shi kuwa mawakin na Buhari Dauda Kahutu Rarara ya ce wasu da ke ɗaukar wannan magana da zafi da yawan su ‘yan ‘good evening ne’ wato dai ‘yan ta more ne, amma ba su san da wancan zancen ba.
” An samu wani lokaci da Buhari ke buƙatar taimako kuma akwai ‘yan arewa da suke da halin da za su taimaka masa amma suka ƙi taimakonsa sai shi Bola Tinubu ɗin ne ya taimaki Buhari kuma ya samu abinda yake so” in ji shi.
Saboda haka a cewar Rarara babu wanda ya isa ya ce Bola Tinubu bai taimaki Buhari ba kuma shi Buharin ya sani, ya ce hatta mu ɗin nan mun sani.
Ya kara da cewa shi Bola Tinubu abokin siyasar Buhari ne, ya taimaki Buhari ya zama ɗan takara kuma yai zo ya taimaka aka kafa gwamnati da shi.
A cewar Rarara baban abinda zai yi na nunawa arewa dattako shi ne, ko dai ya goyi bayan Tinubu ko kuma ya bada dama ga kowa da kowa ya shiga zaɓen fidda gwani wanda Allah ya ba shikenan.