Tsohon dan takarar kujerar majalisar dokokin Jihar Kano, Honarabul Aminu Abukakar Boyi ya bayyana cewa masu kulle-kullen sauya takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2027, da cewa suna gayyato wa APC fadiwa kasa warwas.
Honarabul Aminu na wannan jawabi ne a lokacin da yake tsokaci kan wasu zarge-zarge da suka fara bankadowa na yunkurin sauya wanda zai wa jam’iyyar APC takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a 2027.
- Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)
- Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
Ya ce Kashim Shettima da Bola Tunibu dan juma ne da dan jummai, don haka nasarar jam’iyyar APC ita ce a tabbatar da takarar Tinubu tare da Shettima.
“Muna tabbatar wa da APC cewa matasan yankin arewa gaba dayansu Kashim Shettima ne fatansu, don haka duk wani mai yunkurin kishiyar haka na iya kai matasa da masu kishin yankin arewa bango.
“Shettima mutun ne na matasa kuma mai kishin wannan yankin namu, wannan tasa matasa muka yanke hukuncin ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da ganin ba wanda ya yi gangancin taba kimarsa.”
Aminu Boyi ya kara da cewa ido ba mudu ya san kima, idan dai batun nagarta da kwarewa da jajircewa, lallai Shettima ya yi zarra, wannan tasa ba za su laminci wani ya sauya sunansa ba a takatar 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp