• English
  • Business News
Tuesday, June 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya

by Sulaiman
2 days ago
in Labarai
0
Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa yaɗa labaran da ke nuna nasarorin da Nijeriya ta samu a tsarin mulkin dimokiraɗiyya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin bikin cikar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) shekaru 70 da kafuwa, wanda aka gudanar a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.

  • Matsalolin Rayuwa: Matasan Suleja Na Buƙatar Ƙarfafa Gwuiwa
  • Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli

Bikin ya kuma haɗa da karramawa da ƙaddamar da wani littafi na tarihin ƙungiyar.

Da yake jawabi a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin Babban Baƙon Taron, kana kuma a matsayin Jagoran Biki, Ministan ya jaddada kusanci da goyon bayan da Shugaba Tinubu yake da shi ga kafafen yaɗa labarai a ƙasar nan.

Ya ce: “Tun daga lokacin da ya kasance cikin masu gwagwarmayar tabbatar da zaɓen 12 ga Yuni tare da jarumai daga cikin ‘yan jarida, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa dangantaka mai ƙarfi da kafafen yaɗa labarai wanda ba a taɓa ganin makamancin sa a tarihin shugabannin Nijeriya ba.”

Labarai Masu Nasaba

An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya.

“Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi.

Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya mai ma’ana, hakan zai taimaka wajen girmama sadaukarwar da ta haifar da dimokiraɗiyyar Nijeriya tare da ƙarfafa haɗin kan ƙasa da amincewar jama’a da gwamnati.

Ya ƙara da cewa, “Ta yin hakan, kafafen yaɗa labarai suna tabbatar da matsayin su a matsayin ginshiƙi wajen ɗorewa da ƙarfafa tafarkin dimokiraɗiyyar Nijeriya.”

Ya kuma sake tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu tana da cikakken niyyar kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da ‘yancin kafafen yaɗa labarai.

“Na sha faɗa a wurare da dama, kuma zan sake faɗa a nan, cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai a matsayin ginshiƙi kuma tushen dimokiraɗiyyar Nijeriya.

“Za mu ci gaba da ƙarfafa manufofi da shirye-shiryen da za su ba kafafen damar bunƙasa wajen cika nauyin da ya rataya a wuyan su ga dimokiraɗiyya da al’umma,” inji shi.

Ya kuma taɓo ƙalubalen da ‘yan jarida suke fuskanta a wannan zamani na dijital, ciki har da tasirin Ƙirƙirarrar Basira (AI), yaɗuwar labaran ƙarya da rawar da jaridar jama’a ke takawa.

“Bayyanar Ƙirƙirarrar Basira (generative AI) cikin ‘yan shekarun nan ta ƙara dagula lamarin, inda ake cika mu da hotuna da bidiyo na bogi da yaɗa labaran ƙarya, wanda ya sa aikin jarida na gaskiya ya fi wuya, amma kuma ya fi zama wajibi fiye da da,” inji shi.

Ministan ya bayyana cewa ana nan ana aiki tare da UNESCO domin kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai (MIL) ta musamman a Abuja.

“Shi ya sa muke haɗa gwiwa da UNESCO wajen kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai (MIL) a nan Abuja, wacce za ta zama ta farko irin ta a duniya. Da zarar ta fara aiki, wannan cibiyar za ta zama wani babban tushe wajen inganta aikin jarida na gaskiya a Nijeriya,” inji shi.

Idris ya kuma bayyana shirye-shiryen gwamnatin Tinubu na haɗa kai da NUJ wajen fuskantar muhimman matsalolin aikin jarida da suka haɗa da walwalar ma’aikata, daidaiton jinsi, da sauya fasalin aiki zuwa tsarin zamani.

“Muna da niyyar aiki tare da ku da kuma tallafa maku wajen fuskantar waɗannan matsaloli yayin da kuke ƙoƙarin daidaita kan ku da sabon yanayin ƙarni na 21,” inji shi.

Yayin da ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan ayyukan kafafen yaɗa labarai shi ne sa ido kan ayyukan gwamnati, Ministan ya buƙace su da su riƙa kallon gwamnati a matsayin abokiyar aiki wajen gina Nijeriya mai zaman lafiya da cigaba.

“Ko da yake kuna da rawar da kuke takawa wajen sa ido a kan gwamnati – kuma muna maraba da hakan – akwai buƙatar ku riƙa kallon mu a matsayin abokan aiki, kuma masu haɗa kai wajen samar da zaman lafiya, tsaro da cigaba da ƙasar nan ke nema ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu,” inji ministan.

Ya kuma taya NUJ murna kan cikar ta shekaru 70 da kafuwa tare da yaba wa ƙungiyar kan ƙaddamar da wani littafi da ke bayyana tarihin ta.

“Ina da yaƙinin cewa aikin jarida yana da buƙatar ko yaushe ya riƙa bayyana labaran sa da kan sa da kuma tsara yadda za a bayyana shi; domin ba wani zai yi mana hakan ba,” inji shi.

Idris ya kuma yaba da girmamawa ga Shugaban Taron, Cif Aremu Olusegun Osoba, da kuma Mamallakin jaridar Vanguard, Mista Sam Amuka-Pemu, bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar a harkar jarida da hidima ga jama’a, yana mai cewa su ne abin koyi a wannan sana’ar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Matsalolin Rayuwa: Matasan Suleja Na Buƙatar Ƙarfafa Gwuiwa

Next Post

Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?

Related

An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani
Manyan Labarai

An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

38 minutes ago
Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3
Manyan Labarai

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

3 hours ago
Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump
Kasashen Ketare

Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

4 hours ago
Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

11 hours ago
EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2
Labarai

EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

11 hours ago
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga
Labarai

Gargaɗin Amurka: Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja

13 hours ago
Next Post
Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?

Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra'ila?

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

June 24, 2025
Manchester United Za Ta Biya Fam Miliyan 60 Don Ɗaukar Mbeumo Daga Brentford

Manchester United Za Ta Biya Fam Miliyan 60 Don Ɗaukar Mbeumo Daga Brentford

June 24, 2025
Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

June 24, 2025
Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

June 24, 2025
Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

June 23, 2025
EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

June 23, 2025
Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

June 23, 2025
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

Gargaɗin Amurka: Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja

June 23, 2025
Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

June 23, 2025
An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027

An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027

June 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.