Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya kuma ɗan jihar Kebbi, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana mai cewa matakin ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma nazari na ƙashin kai. A wata sanarwa da ya fitar ranar 2 ga Yuli, 2025, Malami ya bayyana komawarsa jam’iyyar ADC – jam’iyyar da ke jagorantar sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa.
Malami ya ce ba fushi ko son mulki ne ya jawo masa wannan mataki ba, illa kawai damuwa da ƙaunar ƙasa da kuma wahalhalun da al’ummar Nijeriya ke ciki. Ya bayyana cewa Nijeriya na cikin mawuyacin hali, inda rashin tsaro ya yi kamari, musamman a Arewacin ƙasa, yayin da gwamnati ke fifita siyasa akan tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
- Fitaccen Malamin Musulunci Mai Da’awar Sunnah A Nijeriya, Dr. Idris Dutsen Tanshi Ya Rasu
- Tarihin Makarantar Katsina-kwalej Zuwa Ta Horon Malamai (1)
Ya kuma caccaki halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, yana mai cewa hauhawar farashin kayan masarufi da rashin aikin yi sun kai matakin da talakawa ba sa iya ciyar da iyalansu. Ya zargi gwamnati da watsi da shugabanci, inda ya ce rabon muƙamai da aiwatar da manufofi yanzu yana bisa biyayya ta siyasa, ba ƙaunar ƙasa ba.
A ƙarshe, Malami ya ce matakin da ya ɗauka na komawa ADC wata hanya ce ta dawo da adalci, da cancanta, da haɗin kai da farfado da ƙasa.
Ya tabbatar wa mutanen jihar Kebbi da cewa zai ci gaba da kasancewa da su, yana kare muradunsu da muradun Nijeriya gaba ɗaya. Ya yi kira ga ’yan Nijeriya su haɗu don ceto ƙasar daga durƙushewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp