Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wanda ya bata wa Gwamna Wike na Jihar Ribas rai, inda ya yi karin haske kan yadda jam’iyyar PDP ya zabi Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Lamido ya yi tsokaci kan rigimar da ke tsakanin Atiku da Wike a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
- Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba – Kwankwaso
- Wayar Salula Ta Haddasa Gobara A Gidan Mai A Legas
Ya ce, “Wannan jam’iyya kamar kowace jam’iyya a Nijeriya tana da tsarin mulkinta, ka’idoji da tsare-tsare kuma idan aka duba tsarin da PDP ke yi tun daga matsayin mai ba da shawara har zuwa shugaban majalisar wakilai, Gwamna, Majalisar Dokoki ta Kasa akwai tsare-tsaren da duk majalisa ce ke samar da kowane mataki.
“Mutane sun nemi takara; wasu sun yi nasara, wasu kuma sun fadi. Haka kuma a matsayin shugaba da gwamna. To mene ne abun bacin rai game da Wike? A gani na waye ya yi wa Wike laifi? Wane ya bata masa rai? Babu wannan batun. A babban taron jam’iyya da aka yi a Abuja Wike da kansa ya ce an yi sabihin zabe. To mene ne abun bacin rai? Wane ne ya yi laifi? Ina so in sani da farko saboda me yasa Wike ke kawo batun nan?
“Taron ya fitar da dan takara wanda ya lashe zaben fidda-gwani. Idan akwai kuskure taron ne ya bata wa Wike rai, ba kuma shugaban jam’iyya ba.”
Lamido ya bayyana cewa, Wike ba shi da ikon juya siyasa a Jihar Ribas saboda yana matsayin gwamna.
Ya kara da cewa, “Wike mutum ne. Ba na jin saboda shi gwamna ne zai juya mutann Ribas. Mutanen Ribas da dama na yin PDP tun 1999. Ba zai yiwu ya juya yadda yake so ba saboda shi gwamna ne; hakan ba zai iya aiki ba.”