Gwamnatin Jihar Kano ta samu babban nasara a yaƙi da safarar magunguna na bogi, inda aka kama jabun magunguna da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 1.3 a wata sabuwar nasara da aka samu ta hanyar Kanawa Pharmaceutical Coordinated Wholesale Centre (KPP-CWC) da ke cikin Kano Economic City, Dangwaura, kan hanyar Zaria.
A taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, Hajiya Furera Ado Muhammed, babbar jami’ar harhaɗa magunguna a cibiyar, ta bayyana cewa wannan kamen ya biyo bayan sahihin bincike da kuma tsauraran matakan da aka ɗauka tun bayan da aka rufe kasuwar sayar da magunguna ba bisa ƙa’ida ba aka kuma mayar da ita zuwa wannan sabon wurin.
- Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya
- Ahmed Musa Ya Ƙaryata Kyautar Motoci Ga Ƴan Wasa Da Ma’aikatan Kano Pillars
A cewar Furera, cikin samfuran da aka yi wa gwaji don gano sinadaran aiki (AIC), kusan kashi 40.3% na magungunan—musamman antimalaria, da antibiotics da kuma painkillers da ake amfani da su wajen jinyar yara—sun gaza gwajin kuma sun nuna cewa ba su da inganci. Ta ce irin waɗannan magunguna da ake yawan amfani da su ne ke haddasa gazawar warkewa da asarar rayuka.
Tuni dai aka miƙa jabun magungunan da aka kama, waɗanda aka ƙiyasta kuɗinsu ya kai N1.3bn, ga Kwamitin Jihar Kano kan yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi domin a lalata su.
Ta yaba wa gwamnatin tarayya da jagororin hukumomin da ke kula da harhaɗa magunguna—kamar su Pharmacy Council of Nigeria (PCN) da NAFDAC—kan goyon bayan da suka bayar wajen tabbatar da cewa cibiyar KPP-CWC ta zama abar koyi ga sauran jihohin ƙasar. Ta kuma buƙaci ƙara wayar da kan jama’a domin tabbatar da ci gaba da bin doka da oda wajen harkar sayar da magunguna a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp