Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, kasar Sin tana goyon bayan kungiyar G20 a matsayin wani muhimmin dandali na hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa, kuma tana ci gaba da taka rawar gani wajen karfafa cudanyar bangarori daban daban, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin taron menama labarai na yau da kullum, lokacin da take tsokaci game da taron ministocin kudi da na shugabannin manyan bankunan kasashen kungiyar G20 da za a yi a kasar Afirka ta Kudu a mako mai zuwa.
- FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Dangane da furucin da Amurka ta yi cewa za ta kakaba wa Brazil haraji mai yawa da ya kai kashi 50 bisa dari, Mao Ning ta ce bai kamata haraji ya zama wani makami na tilastawa ko cin zarafi da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe ba.
Game da bukatar da Amurka ta gabatar ta neman kasar Koriya ta Kudu ta dauki matakai don dakile kasar Sin yayin tattaunawar cinikayya tsakaninta da Koriya ta Kudu, Mao Ning ta ce, bai dace yarjejeniya da tattaunawa tsakanin kasa da kasa ta mayar da hankali ga cutar da moriyar wasu bangarori na waje ba.
Da ta tabo batun ziyara ta baya-bayan nan da firaministan kasar Sin Li Qiang ya kai kasar Masar, Mao Ning ta bayyana cewa, a yayin ziyarar, firaministan na Sin da takwaransa na Masar sun shaida rattaba hannu kan wasu takardun hadin gwiwa a fannonin cinikayya ta yanar gizo, da samun ci gaba mai rage fitar da hayaki mai dumama yanayi, da taimakon raya kasa, da harkokin kudi, da kiwon lafiya.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp