Jigida kamar yadda aka fi saninta a Hausance wata damarace da mata suke daurawa a kugunsu.
Ita dai jidiga ada anayinta ne da dutse na tsakiya ga masu hali, su kuma talakawa ana yi musu tasu da wata roba mai dauke da launuka daban-daban domin karawa abin kyau da armashi a idanuwan mai kallo.
- Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
- Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da MasarÂ
Larabawa da Indiyawa su ne suka fi amfani da jigida tun tuni kamar yadda bincke ya nuna. Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da yanayin yadda suke rawar al’adarsu in dai suka kada da kuma girgiza kugunsu jigida na aman sauti tana hawa tana sauka.
Sai dai a baya kabilu da daman gaske na Africa suna amfani da jigida sosai fiye da yadda Larabawa da Indiyawa suke yi ganin yadda su bakaken Afirka suka maida jigida cikin wasu jerin al’adunsu da kuma camfe-camfe irin nasu.
Wasu daga camfin da aka yi wa Jigida a Afirka shi ne, yana taimaka wa mata masu ciki sauki wajen haihuwa, haka nan kuma budurwa da take sanya jigida tafi saurin sa’ar aure da wuri. Hakan kuma duk macen dake sanya jigida aljanu ko wasu abubuwa na sammu ba za su kamata ba a camfin wasu kabilun na Afirka.
Ita jigida irin ta da ba haka kawai ake sakata ba, domin shahararru kuma jarumai ne a wacan lokacin suke yin ta don haka ne take da tasiri da kuma tsada ga masu saye.
Sai dai a baya akwai jigida ta ‘yan mata akwai ta matan aure da kuma na tsofaffi, kuma a wannan lokacin babu matsala ko wani gani-gani da ake yi wa macen da aka ganta sanye da jigida saboda abu ne da aka dauka na al’ada maimakon ado ko kiran maza da wasu ke ganin matan yanzu suke yi da jigida ba.
Yanzu dai sanya jigida ga mata ya bunkasa ya fadada har cikin kashen Turai. Matan turawa kamar yadda bincike ya tabbatar kashi 60 cikin 100 suna sawa.
Sai dai a wannan zamanin da muke ciki sanya jigida ga mata ya zama abin ado ne ba domin dalilai irin na camfi da muka ambata a baya da mutanen baya suke yi ba, duk da yake ana samun kadan daga cikin matan kauyawa masu saka jigida da manufa ta camfi.
Shima dai kamar irin na da ne, wannan zamanin ana yin jigida ne da wasu duwatsu masu kyalli da kuma robobi masu sheki wadanda nauyinsu bai kai irin na zamanin baya ba.
Babban alfanun da jigida yake yi wa mata kamar yadda bincike ya tabbatar a wannan lokacin shi ne, yana kara wa mace fadin kugunta ga irin matan nan da suke da karancisa.
Maza da dama da aka zanta da su sun nuna sha’awarsu ta ganin matansu na aure suna saka jigida domin yana karamusu kyau musamman idan mace tana sanye da kayan da za su bayyanasu.
Har ilayau cikin alfanun da jigida ke da shi shi ne ta kan motsa sha’awan maza a yayin da suka ji sautinsa ko suka hango shatinsa.
Sai dai duk da wadannan tasiri, mahimanci da alfanun da jigida ke da su ba duka mata bane suke sanyawa ba, haka ma maza da dama ba su son ganin mace da jigida. Wasu mutane sun riga sun kudura cewa duk mace ko budurwar da aka ga tana sa jigida ko aka ji sautinsa a tare da ita suna daukan irin wadannan matan mazinata ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp