Rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a wani asibiti da ke Birnin London inda yake jinya.
Kamar yadda Empowered Newswire ta Tsohon shugaban ƙasar ya kwana biyu yana fama da rashin lafiya wanda hakan ya sa Shugaba Bola Tinubu, ya aika mataimakinsa don binciko masa yanayin jikin dukda ana ganin yana samun sauƙi a halin yanzu.
- Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Shettima, ya zarce wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a birnin na London ne daga Addis Ababa na Habasha, bayan amsa gayyatar Firayim Minista Abiy Ahmed Ali don halartar ƙaddamar da shirin Green Legacy Initiative (GLI) na ƙasashen Gabashin Afirka.
Majiyar ta ce Shettima ya isar da saƙon Tinubu ga Buhari, tare da tabbatar da cewa an ba shi goyon baya har zuwa samun lafiya.
Mai magana da yawun Shettima, Stanley Nkwocha, ya shaida da cewa mai gidansa ya kai ziyara birnin London amma bai bayar da tabbacin komai game da manufar ziyarar ba don wanda ya ce bai da cikakken jadawalin tafiyar ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp