Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya nuna matuƙar kaɗuwar sa bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne yau a Ladan bayan ya yi fama da rashin lafiya.
- Cinikayyar Shige Da Fice Ta Sin Ta Karu Da Kaso 2.9 Bisa Dari A Watanni Shida Na Farkon Bana
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Talata A Matsayin Hutu Don Alhinin Marigayi Buhari
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa wannan lokaci na rasuwar tsohon shugaban ƙasan, wani mummunan yanayi ne a duk faɗin ƙasar nan.
Sanarwar ta ce, “Rashin tsohon shugaba Muhammadu Buhari, rashi ne mai zafi ga duk ‘yan Nijeriya.
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Zamfara, muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga iyalan tsohon shugaban.
“Allah gafarta masa kurakuran sa, ya sa aljanna ce makomar sa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp