Tsohon mai bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan da ya ce da Buhari ya dogara da asibitocin Nijeriya, da ya daɗe da rasuwa.
Adesina ya faɗi haka ne a wani shiri na musamman a gidan talabijin na Channels da aka gabatar domin tunawa da Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti da ke Landan a ranar Lahadi.
- HOTUNA: An Tsaurara Tsaro A Gidan Buhari Da Ke Daura
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha
Wasu sun soki yadda Buhari ke yawan zuwa ƙasashen waje domin neman lafiya.
Amma Adesina ya kare shi, inda ya bayyana cewa Buhari ya daɗe yana zuwa asibiti a Landan tun kafin ya zama shugaban ƙasa a 2015.
“Likitocin can sun san rashin lafiyarsa sosai,” in ji Adesina.
“Ba saboda wasa yake zuwa can ba, ya yarda da su, kuma sun san yadda za su kula da shi.”
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin asibitocin Nijeriya ba su da kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata da za su iya kula da lafiyar Buhari.
“In da ya dogara da wasu asibitocinmu, wataƙila da tuni ya riga mu gidan gaskiya,” in ji shi.
Wannan furuci ya ƙara jawo muhawara a faɗin ƙasar game da halin da harkar kiwon lafiya na Nijeriya ke ciki, da kuma yadda manyan ‘yan siyasa ke fita ƙetare don neman magani.
Buhari, ya shugabanci Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023.
A lokacin mulkinsa, musamman a shekarun farko, ya sha zuwa ƙasar Birtaniya domin neman lafiya, amma ba a taɓa bayyana cutar da ke damunsa ba.
Ya rasu ne a wani asibiti da ke Landan a ƙarshen mako, kuma mutuwarsa ta haifar da muhawara a faɗin ƙasar.
Za a gudanar da jana’izarsa a ranar Talata a Daura, a Jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp