Peter Obi, É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar LP a zaÉ“en 2023, ya ziyarci Daura a Jihar Katsina domin yi wa iyalan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta’aziyya.
Obi, ya ziyarci gidan Buhari a Daura, kwana guda bayan da aka binne tsohon shugaban ƙasar a garinsu.
- Omokri Da Sarki Sun Soki Obi Saboda Rashin Halartar Jana’izar Buhari
- Yara 2 Sun Kuɓuta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno
Buhari, wanda ya shugabanci Nijeriya a matsayin soja da kuma mulkin farar hula, an binne shi ne a ranar Talata.
Limamin Babban Masallacin Juma’a na Daura, Sheikh Salisu Rabiu ne, ya jagoranci sallar jana’izar, sannan aka binne shi da misalin ƙarfe 5:50 na yamma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp