Fitaccen ɗan jaridar nan kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, ya bayyana cewa ya fice daga Jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar ADC.
A cikin wata wasiƙar da ya rubuta a ranar 17 ga watan Yuli, 2025, wacce ya aike wa Shugaban PDP na mazaɓar Ihievbe, ƙaramar hukumar Owan East ta Jihar Edo.
- Gwamna Lawal Ya Bai Wa Dalibai Sama Da 8,000 Tallafi A Zamfara
- Buhari Ya Taimake Ni Lokacin Da Wasu Ke Ƙoƙarin Ruguza Majalisar Tarayya — Gbajabiamila
Momodu ya ce ya fice daga jam’iyyar ne saboda ta faɗa hannun masu adawa da dimokuraɗiyya.
Ya bayyana cewa yanzu zai mara wa jam’iyyar ADC baya, wacce ke son ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
“Ina sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar PDP daga yau,” in ji shi.
“Dalilina kuwa yana da sauƙi. Jam’iyyar ta faɗa hannun masu adawa da dimokuraɗiyya.
“Saboda haka, abin da ya dace shi ne a bar musu ragowar jam’iyyar, yayin da mu da yawa za mu koma sabuwar jam’iyyar haɗaka mai suna ADC.”
A farkon wannan wata, Momodu ya zargi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da yi wa jam’iyyar APC aiki a ɓoye duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar PDP a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce: “Ba tare da wata shakka ba, mutane suna bar wa Wike da abokan aikinsa PDP. Wannan lamari an riga an hango shi. Jam’iyyar APC mai mulki tana shigar da mutanenta a manyan jam’iyyun adawa don tarwatsa su.”
Haka kuma, Momodu ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu, yana cewa tana ƙara jefa rayuwar ‘yan Nijeriya cikin ƙunci fiye da yadda aka gani a lokacin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
“Shin wannan ita ce Nijeriya da kuke mafarki? Rayuwarku ta fi ta da sauƙi ne fiye da shekaru biyu da suka wuce? Ko da Buhari ya tafi, mun ga abin da ya bari, amma yanzu lamarin ya ƙara muni,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp