Sauye-sauyen da ake gani a wani lungu na wani birni ya kan iya nuna ci gaban da daukacin wata kasa ta samu.
Misali, a yau na raka wani abokina dan Najeriya zuwa ofishin hukumar shige da fice ta birnin Beijing na kasar Sin, domin kula da wasu harkoki, sai na tarar da yadda hukumar ta kaura zuwa wani sabon gini da aka kammala, mai taken “Cibiyar Hidimomin Gwamnati”. A wurin, ana iya kammala ayyukan da suka shafi hidimomi na gwamnati nau’ika sama da 1,900 cikin sauri, ta hanyar nemo tagar da ta dace, da aka kebe wa masu bukatar daidaita mabambantan harkoki. Wato yanzu babu bukatar yin kai-komo tsakanin hukumomi daban-daban, kamar yadda a kan yi a wasu lokuta a baya.
- Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato
- Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa
Bari in yi muku karin haske kan taken wannan bayani: “Tsayi” na nufin manyan gine-gine da suke nuna yanayin ci gaba na wani birni, da habakar tattalin arzikinsa. Kana “zafi” a nan ba ya nufin yanayi, maimakon haka yana nufin jin dadi da gamsuwar mutanen da ke zaune a cikin birnin. Kula da wadannan bangarori guda biyu yadda ya kamata, shi ne umarnin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar wa jami’ai masu kula da birane 694 na kasar.
A yau da ni da abokina mun gama ayyukanmu cikin sauri, mun fito daga Cibiyar Hidimomin Gwamnati, sa’an nan mun waiwayi baya, mun ga cikakken tsarin wannan babban gini mai salon zamani. Abun da muke ji shi ne: Beijing ta samu karin ci gaba. A lokacin, mun shaida “tsayi” na ci gaban birnin Beijing, da kuma “zafi” na birnin a cikin zukatanmu.
Wani taro da ya gudana a baya-bayan nan game da aikin raya birane a kasar Sin, ya ta’allaka ne kan manufar “amfani da tsare-tsaren birane wajen samar da hidimomi ga jama’a”, tare da ba da shawarar raya biranen kasar, don su zama masu sabbin fasahohin da aka kirkira, da ingancin muhallin rayuwa, da kyan gani, da iya tinkarar bala’i, da wayewar kai, gami da basira. Alal hakika, tun tuni an riga an fara aiwatar da wadannan ra’ayoyi a biranen Sin: Tun daga shekarar 2019 har zuwa yanzu, kasar Sin ta kammala aikin gyaran tsoffin ungwanni kusan 280,000, da kafa na’urorin lif sama da 130,000, da gina karin wuraren ajiye motoci miliyan 3.8, da sabbin filayen motsa jiki da fadinsu ya kai murabba’in mita miliyan 31.
Har ila yau, Sinawa sun yada irin wannan ra’ayi na raya birane don bautawa jama’a, zuwa nahiyar Afirka . Misali, a Lagos na Najeriya, layin dogo na “Blue Line” da wani kamfanin kasar Sin ya gina ya takaita lokacin zirga-zirgar jama’a da dama, daga minti 90 zuwa minti 20. Kana a birnin Lusaka na kasar Zambia, tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da wani kamfanin Sin ya gina, ta sa an samu karin hasken fitilu, a shaguna daban daban dake kan titunan birnin a cikin dare.
Ban da haka, a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, aikin kwaskwarima da kamfanonin kasar Sin suka gudanar, sun mayar da wani kango cike da laka zuwa daya daga cikin filayen wasa mafi girma da inganci da ake samu a cikin biranen Afirka.
“Ya kamata a tabbatar da ‘tsayi’, gami da ‘zafi’, yayin da ake raya wani birni.” Bari mu tuna da wannan magana ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, mu kuma shaida yadda sannu a hankali ta zama gaskiya a birane daban daban na kasar Sin da na kasashen Afirka. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp