Sabon shugaban riko na kungiyar masu shirya fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Shehu Hassan Kano ya bayyana cewa; yanzu lokaci ne da ya kamata masana’antar Kannywood ta hada kai da ‘yan siyasa, musamman wadanda ke rike da mulki; domin sama wa masana’antar ci gaba mai dorewa, a wata hira da ya yi da FIM, Shehu Hassan, wanda shi ne ya maye gurbin tsohon shugaban kungiyar, Malam Mai Kudi (Cashman), wanda ya rasu a kwanakin baya ya bayyana cewa; kowa da kowa nasu ne a MOPPAN.
“Ba jam’iyya za mu shiga ba, ba kuma wani bangare na siyasa za mu yi ba, ita masana’antar Kannywood, akwai ‘yan siyasa, kuma ba jam’iyya daya suke yi ba, za ka ga wasu suna wannan jam’iyar; yayin da wasu kuma za su zabi wata jam’iyyar daban, don haka, mu a tsarinmu na MOPPAN, kowa namu ne, dan masana’antarmu ne, duk wanda ya ga akwai wani abu da za a yi harkar fim ta ci gaba, ya kawo mana shi, mu nan a kungiyance za mu shige gaba wajen ganin wannan abu ya tabbata”, in ji Hassan Kano.
- Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?
- Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)
Har ila yau, ya ci gaba da bayyana cewa; don haka, mu ba wani bangare guda daya za mu bi mu rike ba, domin kuwa yin hakan; akwai hadari, so muke in dai dan fim ne, duk wata tafiya da yake yi ta siyasa; ya zamana ya amfana da tafiyar, ita ma masana’antar ta amfana, ko da kuwa ba jam’iyyarsa ba ce take mulki, za mu hadu ne a matsayin ‘yan fim mu amfana da junanmu a wajen tafiyar siyasa.
Wannnan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara kada gangar siyasa a Nijeriya, kwanaki dai an hangi wasu jarumai a masana’antar Kannywood, sun kai ziyara har gida ga tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP, a babban zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa).
Hakan yasa wasu ke ganin hakan bai dace ba, ganin cewa; Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta bugi kirjin yi wa masana’antar Kannywood gata, ta hanyar bai wa wasu daga cikin jaruman masana’antar Kannywood manya-manyan mukamai a gwamnati, ciki har da Babban Manajin Darakta na Hukumar Fina-finai ta Nijeriya (NFC).
Koma dai mene ne, Shehu Hassan Kano ya ce; ba za su takurawa kowa a cikin ‘yan kungiyar ta MOPPAN, wajen yin ra’ayin siyasar da suka ga dama ba, sai dai, ya ce duk wanda zai yi siyasa ya fara dubawa idan akwai mafita, sai ya shiga idan kuma babu sai ya hakura ya canza wata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp