ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Amurka

A baya-bayan nan ne dai ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya fito fili ya bayyana cewa, Amurka na yin matsin lamba ga kasashen Afirka, don su karbi bakin hauren da Amurka ta kora daga cikin gidanta. Inda Najeriya, a bisa matsayinta na wata babbar kasa, ta daure da matsin lambar, kuma ta ce “A’a” ga Amurka. Sai dai ga wasu kasashe masu raunin tattalin arziki, da suke fuskantar matsin lamba daga Amurka, yawancinsu ba su da wani zabi illa mika wuya.

A cewar gidan telabijin na CNN, a kwanan baya kasar Amurka ta kori bakin haure biyar, ‘yan kasashen Jamaica, Laos, Cuba, Yemen da Vietnam, wadanda ake zargi da aikata manyan laifuffuka a kasar. Sa’an nan ta tusa keyarsu zuwa kasar da take wa lakabin “kasa ta uku mai tsaro”, wato kasar Eswatini dake kudancin nahiyar Afirka. Wannan lamari dai ya haifar da fushi mai tsanani a tsakanin al’ummar Eswatini. Har ma jam’iyyar adawa ta kasar, PUDEMO, ta ce karbar wadannan bakin haure da Amurka ta kora “yana da babbar barazana ga al’ummar Eswatini, wadanda da ma sun kasance cikin yanayi mai rauni.”

  • An Samu Rarrabuwar Kai Kan Makin Shiga Manyan Makarantu
  • Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Ragu A Nijeriya

Abin da ya ba ni sha’awa a cikin wannan al’amari shi ne sunan da Amurka ta lakaba wa Eswatini, wato “kasa ta uku mai tsaro”. A cewar wasu takardun bayani na kungiyar kasashen Turai ta EU, kukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta taba jaddada cewa, ya kamata a sami “alaka mai ma’ana” tsakanin “kasa ta uku mai tsaro” da ‘yan gudun hijira masu neman mafaka, misali, dangin da ke zaune a kasar. Bugu da kari, ya kamata “kasa ta uku mai tsaro” ta tabbatar da cewa ‘yan gudun hijirar sun sami cikakkiyar kariya a cikin yankunanta.

ADVERTISEMENT

Bisa ga wannan ma’auni, bai kamata a dora Eswatini a matsayin “kasa ta uku mai tsaro” ba. Saboda, da farko, babu wata “alaka mai ma’ana” tsakanin mutanen biyar da kasar Eswatini. Na biyu, da alama kasar ba za ta iya ba wa wadannan mutane “cikakkiyar kariya” ba. Bisa wani rahoton batun kare hakkin dan Adam na kasar Eswatini da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar, an ce akwai lamarin “aikata hukuncin kisa ba bisa doka ba” da “hukunce-hukunce na zalunci” da suka afku a kasar, kuma gidajen yarin kasar na fuskantar matsalolin “cunkoso, da lalacewar kayayyaki, da rashin abinci mai gina jiki, da yawan samun fadace-fadace tsakanin fursunoni.”

Amma duk da haka kasar Amurka ta mai da Eswatini a matsayin “kasa ta uku mai tsaro”. Saboda me? Dalili na farko shi ne domin kasar Amurka ta ga yana da sauki a sarrafa wata karamar kasa, wadda za ta karbi bakin hauren da aka kora, bayan an dan matsa mata lamba. Bugu da kari, wata takardar gwamnati da jaridar Washington Post ta nuna wa jama’a ta shaida ce, watakila da gangan ne gwamnatin Amurka ke korar bakin haure zuwa kasashen da ba a samun cikakken hakkin dan Adam. Ta haka ne gwamnatin Amurka ke fatan tilasta wa bakin haure don su bar kasar da kansu, in ba haka ba za a iya korarsu zuwa Eswatini, ko kuma Sudan ta Kudu da ke fama da tashin hankali, har ma za a iya kulle su a rumbun ajiyar kaya na wani sansanin sojan Amurka dake nahiyar Afirka (wani abu da ya taba faruwa a kasar Djibouti a baya-bayan nan) .

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Ana iya takaita halin Amurka game da wannan al’amari da kalma daya: Maras kulawa. Saboda kasar ba ta damu da nauyin da ke kanta bisa la’akari da matsayinta na babbar kasa ba, balle ma dangantakar diflomasiyya, da adalci, da hakkin bil’adama, da muradu na wasu kasashe. Sai dai abu daya kawai dake janyo hankalinta, wato kokarin cika burin korar baki. Hakika wannan ra’ayi na “Amurka na gaba da kome” da yanayi na son kai sun kasance cikin dukkan manufofin kasar.

Eswatini, wadda Amurka ta manna ta kan matsayin “kasa ta uku mai tsaro” a wannan karo, ba a san irin “yarjejeniya” da ta kulla da Amurka ba. Amma, zai yi matukar wahala Eswatini ta kare muradunta, yayin da take mu’amala da wata babbar kasa kamar Amurka mai matukar son kai. (Bello Wang)

Amurka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka
Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda
  • Sulaiman
    Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa
  • Sulaiman
    Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i

El-Rufai Ya Magantu Kan Abokansa Da Suka Yi Shiru Yayin Da Yake Tsare A Hannun ICPC

September 24, 2026
An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka

An Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama A Zagaye Na 8 Na Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Amurka

September 24, 2026
Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya

Sin Na Aiwatar Da Kwararan Matakan Ingiza Ci Gaban Duniya

September 24, 2026
Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani

Firaministan Sin: Karfafa Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Da Masu Ci Gaba A Fannin Cinikayyar Fasahohin Zamani

September 24, 2026
Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka

Xi Jinping Ya Isa Washington DC Don Ziyarar Aiki a Amurka

September 24, 2026
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanai A Sakkwato

September 24, 2026
Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

September 24, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

September 24, 2026
Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.