Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta zama Sakatariyar ƙungiyar matan gwamnoni masu fafutukar yaƙi da cutar daji ta ƙasa wato First Ladies Against Cancer (FLAC). Wannan naɗin ya biyo bayan amincewar sauran mambobin ƙungiyar bisa la’akari da ƙwazon da Hajiya Huriyya ta nuna a fannin kiwon lafiya da wayar da kai akan cutar Kansa.
Rahoton naɗin ya fito ne daga babban mataimakiyar sadarwa ta Ofishin Uwargidan Gwamna, Rabi’atu Yusuf, inda ta ce Hajiya Huriyya ta taka gagarumar rawa wajen shirin tantancewa da tallafawa mata masu fama da cutar Kansa a Zamfara, ciki har da ɗaukar nauyin fiye da tiyatar mata 100 da kuma bayar da gudunmawar Naira miliyan uku da rabi don kula da masu fama da cutar.
- An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka
- Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari
A sabon muƙaminta, za ta haɗa kai da sauran matan shugabanni a Nijeriya domin ƙarfafa tsare-tsaren yaƙi da cutar Kansa, musamman wajen wayar da kai, da samar da kayan aikin jinya da kuma inganta hanyoyin warkar da masu fama da cutar. An sanar da naɗin nata ne a lokacin wani taro na musamman da FLAC ta shirya a gidan gwamnati na Jihar Imo da ke Asokoro, Abuja.
Shugabar FLAC, Barista Chioma Uzodimma, ta yaba da jajircewar Hajiya Huriyya Dauda, tana mai bayyana wannan mataki a matsayin ci gaba ga yankin Arewa wajen shiga tattaunawa da aiwatar da manufofi na yaƙi da cutar daji a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp