A 2023 Zan Aiwatar Da Mulkin Gaskiya Da Adalci A Sakkwato- Salame

Hon. Abdullahi Balarabe Salame

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Dan Takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a inuwar jam’iyyar APC a zaben 2023, kana Shugaban Kwamitin Yaki Da Fatara a Majalisar Wakilai, Hon. Abdullahi Balarabe Salame ya bayyana cewar zai kawo sauyi mai ma’ana a shugabancin al’umma a Jihar.

Hon. Salame wanda ke wakiltar Gwadabwa/Illela ya ce ba za su aminta da tilastawa ko kakaba ‘yan takarar da jama’a ba su da ra’ayi a kai ba wadanda za a iya kuka da shugabancin su.

Jigon na APC kuma tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Sakkwato ya bayyana hakan ne a jiya a Sakkwato a taron Kananan Hukumomi 23 domin tattaunawa da bitar rajistar jam’iyya da  zaben shugabannin jam’iyya da ke tafe a dukkanin matakai.

“Ko kadan ba za mu sake yadda a shiga daki a tsayar mana da ‘yan takara ba. A 2023 ‘yan takarar da ke kishin jama’a wadanda suka san matsalolin jama’a da hanyoyin magance kawai za mu zaba.”

Ya ce idan ya samu nasarar zama Gwamnan Jihar Sakkwato zai jagoranci samar da ingantaccen sauyi a sha’anin tsaro a Sakkwato wanda musamman ya addabi Gabascin Jihar.

“Za mu fito da hanyoyin da suka kamata domin kawo karshen matsalolin tsaro da suka hana zaman lafiya da kwanciyar hankali. Da yardar Allah a cikin shekara daya za mu kawo karshen wannan gagarumar matsalar.” Ya bayyana.

Salame ya ce burinsu shine a tsayar da ‘yan takara bisa ga cancanta domin raya Jihar Sakkwato a mulkin gaskiya da adalci, kawar da dabanci da bangar siyasa, cusa tarbiya da da’a a tsakanin al’umma.

A jawabinsa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Hon. Aminu Muhammad Achida ya bayyana cewar matsalar siyasar ubangida ita ce babbar matsalar da ke fuskantar kasar nan wadda ya ce mafita kawai a kawo karshen ta.

“Kowane bangare na Jihar Sakkwato ya gudanar da mulki don haka a bisa ga adalci ya kamata mulkin Jihar Sakkwato ya sake komawa Gabascin Sakkwato a 2023.”

Ya ce yankin su na fuskantar gagarumar matsalar tsaro ta yadda ba dare ba rana ake kai farmaki tare da garkuwa da jama’a don haka ya ce wajibi ne su kawo karshen raba arzikinsu biyu domin biyan kudin fansa. Ya ce a yanzu jami’an tsaro ba za su iya kawo karshen matsalar tsaro ba saboda ba a ba su ingantaccin kayan aiki ba.

Exit mobile version