Al’ummar Karamar Hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto ta bukaci gwamanti ta basu ikon mallakar makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga da suka addabe su.
Jama’ar yankin sun ce sun gaji da yadda ‘yan bindigar ke ci gaba da kai masu hari, da kashe masu mutane da kuma garkuwa da wasu, lamarin da ya janyo masu mummunar asara.
- Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
- Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
Sun ce daga cikin garuruwa 17 da Karamar Hukumar Kebbe ke da su, a yanzu ‘yan bindiga sun kori mutane daga garuruwa akalla 11, saboda yawaitar hare-hare.
Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al’ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai makura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba.
Ya ce ”Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ‘yar karamar gona ya sayar, mai dan karamin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi kokari su kare mu.
”Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,” in ji Tukur Muhammad Fakum.
Dangane da halin da irin barnar da ‘yan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ”Babu dai abinci, wanda bai taba kwana masallaci ba ya yi, ka tashi ka tafi garin da ba ka taba kwana ba, ka kwana dole. Bala’in ya baci.”
Ya kuma ce lamarin rusa kusa duk wata harkar tattalin arziki a yankin.
BBC dai ta yi kokari jin halin da ake ciki daga bangaren gwamnati da jami’an tsaro, amma hakan ba ta samu ba.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da matsalar ‘yan bindiga ta addaba sosai a shekarun nan, inda suke aikata barna, musamman a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da kuma Kebbe.
Bayan ‘yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji da suke ayyukan su a jihar, an kuma samu bulluwar mayakan Lakurawa, wata sabuwar kungiyar da masu sharhi a kan harkokin tsaro ke gargadin cewa za ta iya zama sabuwar annoba ga jihar da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.
A jihar Kebbi da ke makwabtaka da Sokoto ma wasu ‘yan bindigar sun kai hari a kan jami’an tsaro, a Garin Dirin Daji da ke Karamar Hukumar Sakaba ta jihar.
Wata mazauniyar garin ta ce ”Sun kai hari a kan sansanin sojoji da na ‘yansanda, wanda ke gadi a sansanin sojojin sun harbe shi, kuma nan take Allah ya mashi cikawa.”
Ta kara da cewa ”Daga baya an turo jami’an tsaro, wadanda suka kawo dauki cikin gaggawa, kuma da alama kura ta lafa.”