Masu casar Shinkafar da ake noma wa cikin kasar nan sun tura sako ga Gwamnatin Tarayya da ta kawo karshen ayyukan masu yin fasa kaurin shigo da Shinkafar ‘yar kasar waje zuwa cikin kasar nan domin a ceto su daga tabka asarar kimanin naira tirilian 3.4 da suka zuba jarinsu a wajen casar Shinkafar da ake noma wa a kasar.
Sun kuma kara yin kira ga Gwamnatin da ta ceto masu naira miliyan 3.2 da suka zuba jari kan kokarin su na rage rashin ayyukan yi a kasar ta hanyar sarrafa Shinkafar ‘yar gida.
Mista Andy Ekwelem, Darakta Janar na kungiyar masu casar Shinkafa ‘yar gida (RIPAN) ne ya yi wannan kiran a makon da ya gabata a hirarsa da manema labarai a Babban Birnin Tarayyar Abuja.
Kungiyar ta RIPAN ta kuma yi kira ga gwamnatin da ta dakile ayyukan na masu fasa kaurin Shinkafar kasar waje zuwa cikin kasar, dilolinta, manyan masu sayen ta sanan kuma a garkame su saboda yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.
A cewar Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem, “ A shekarun baya da suka gabata, babban kalubalen da Masu casar Shinkafa suka fuskanta a a kasar nan shi ne, ayyukan masu yin fasa kaurin Shinkafa kasar waje zuwa cikin kasar nan.”
Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem ya kuma koka da cewa, ayyukan na masu fasa kaurin yana matukar ciwa kungiyar tuwo a kwarya, sai dai, daga baya gwamnatin ta bayar da umarnin a rufe iyakokin kasar nan don kakile ayyukan na masu fasa kaurin Shinkafar zuwa cikin kasar.
Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem ya ci gkba da cewa, “Amma bayan da gwamnatin ta bayar da umarnin a sake bude iyakokin kasar, hakan ya kara janyo masu yin fasa kaurin Shinkafar zuwa cikin kasar nan ci gana da shigoda Shinkfar ‘yar kasar waje, musamman daga kasashen Benin da Jamhuriyar Nijar, inda ya ci gaba cewa, wannan abin a yanzu, babbar damu wa ce, idan aka yi la’akari da yadda a yanzu, masu casar Shinkafar suke casar kasa da yadda suke yi a baya.”
A cewar Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem “Idan aka bari abin ya ci gaba, masu casar Shinkafar ‘yar gida, za su durkushe, ma’aikatan su za su rasa ayyukansu kuma za su tabka asarar jarin da suka zuba a fannin.
Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem ya kara da cewa, daukacin masana’antar ta samar da ayyukan yi na kai tsaye sama da miliyan 13 ga ‘yan Nijeriya, inda ya ci gaba cewa, a kungiyarmu kadai, sun samar da ayyukan ga ‘yan Nijeriya sama da 15,000.
A cewar Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem, akwai kuma kananan masana’antun casar Shinkafa a daukacin fadin kasar da suka kai yawan miliyan 3.2.
Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem, konwacce masana’anta daya, akalla ta dauki ma’aikata sama da dubu biyar, wanannan zai nuna maka a zahiri, irin karfin da masanaantun masu casar Shinkafar suke dashi.
A cewar Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem, ba za mu samu ido masana’antun su durkushe ba, inda ya yi nuni da cewa, rashin tsaro da ya addabi kasar nan duk rashin aikin yi ya janyo hakan.
Da yake yin dogon bayani kan yawan jarin da masana’antun sukan zuba a fannin, inda sakamakon ayyukan na masu fasa kauri zai janyo wa fannin asara Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem ya yi nuni da cewa, idan har gwamnatin tarayya ba ta dauki matakan gaggawa na dakile ayyukan na masu fasa kaurin Shinkafar, masana’antun dake casar Shinkafar a kasar, musamamn kananan, za su durkushe.
Ya sanar da cewa, kafin zuwan gwamnatin tarayya mai ci, akwai manayn masana’antun casar Shinkafa na zamani a kasar kimanin biyar zuwa shida, amma daga shekarar 2016, mun yi wa guda 47 rijista.
Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem ya ci gkba da cewa, akwai kuma manyan masana’antun na zamani kimanin habe almost 60 a Nijeriya.
Darakta Janar na kungiyar Mista Andy Ekwelem ya kara da cewa, Shinkafar ta Kasar waje za ta iya kasance wa hadari ga lafiyar masu amfani dasu ita ganin yadda ta dade a ajiye, inda ya kara da cewa, akwai bukatar Hukumar NAFDAC ta shiga cikin kasuwanni domin ta tabbatar da ba a sayar wa da :yan kasar ba.