Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
Shugaban Gundumar Cocin Katolika na Adamawa kuma shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), reshen jihar, Bishop Stephen Dami Mamza, ya ce a cikin bacci tunanin gina gidaje ga ‘yan gudun hijira ya zo masa.
Bishop Dami Mamza, wanda ke magana da ‘yan jaridu a Yola, ya ce gina gidajen itace hanyar magance matsalar wurin zama da ‘yan gudun hijira 86, da Cocin ya tsogunar dasu a harabar cocin Theresa’s Catholic tun shekarar 2014.
Ya ci gaba da cewa “lokacin da wannan tunanin ya zo min cikin zociyana na kauda kai, gaskiyar magana ina bacci lokacin.
“Na tashi, wata rana na ce ‘yan gudun hijiran da muke kula da sunnan, har zuwa wani lokaci zamu ci gaba da kula da sun? saboda mun gajiya, ma su tallafawa suna cewa yanzu babu ‘yan gudun hijira a Nijeriya” inji Bishop.
Wannan na zuwa daidai lokacin da mai bisharan ke cika shekaru 25 da fara aikin bishara, shekaru 10 a matsayin Bishop na cocin Catholic, ya kuma yiwa Allah godiya bisa nasarorin da ni’imomin da Allah ya mishi, ya yi fatan samun taimakon Allah a cikin aikin taimakawa jama’a a wasu shekarun ma su zuwa.
Ya ce “na kasance fada na tsawon shekaru 25, na yi shekaru 10 a matsayin Bishop, ina yiwa Allah godiya bisa kyautatawa da ni’imomin da yayi mini, ban taba tsammanin zan kasance fada na tsawon shekaru 25 ba.
“Na gudanar da abubuwa da dama, na yi abubuwa masu kyau da inganci bakin kokarina, har yanzu zan ci gaba da aikata wasu muhimman ayyuka kyawawa” inji Mamza.
Ya ce lokacin ‘yan bindigar kungiyar boko haram, su ka mamaye yankunan kananan hukumomi bakwai a arewacin jihar Adamawa, cocin ya shirya saukar da dubban ‘yan gudun hijira daga musulminsu da kirista.
“Lokacin da boko haram su ka mamaye arewacin Adamawa a 2014, mutane da dama sun shigo nan Yola fadar jiha, suna neman tsira da abincin da za su ci, sai muka bude kofofinmu, makarantunmu, babban cocinmu, da duk kayayyakinmu mun budesu.
“Na kuma bada umurnin duk wani mutumin da ya nema a kawoshinan, a kyalesu anan a kuma basu abinci, kayayyaki, kudade da duk wani abu da’ake dashi, da haka muke fara.
“A lokacin da ‘yan bindiga su ka mamaye kananan hukumomi 7 a arewacin Adamawa, a cikin cocin St Theresa’s Cathedral, muna da ‘yan gudun hijira sama da dubu 3 da su ke zaune anan.
“Kuma duk bayan kowace mako guda, mukan samu karin mutane daga makwabta da su ke zuwa su karbi abinci, munyi tsarin iyalai dubu bakwai da dari biyar (7, 500), yadda muka yi a wancan lokacin, bayaga 3000 da mu ke dasu a cikin coci.
“Lamarin Allah a shekarar 2015, an kwato wasu kananan hukumomin, kuma dayawan ‘yan gudun hijiran sun koma gidajensu, abin makinciki wasunsu sun koma kuma sun rasa rayukansu a can.
“Anan ma akwai wadanda aka kashe saboda gidajen da su ke babu tsaro, amma wadanda haryanzu muke dasu a St Theresa’s Cathedral mafiya-yawansu mutanen da su ke mazauna wuraren da ke kusa da Sambisa ne, komawarsu yana da hadari.
“Hakan ya sa mu ka ce idan su na bukatar su ci gaba da zama anan, za mu kyalesu su ci gaba da zama tun daga 2014 zuwa wannan lokacin, da muke fatan da taimakon Allah za mu maishesu gidajensu.
“Yanzu muna shirin maishe da ‘yan gudun hijira magidanta 86, muna kuma da wasun da za mu ci gaba da daukan nauyin abincinsu” inji Bishop Dami.
Dakta Stephen Mamza, wanda ya godiwa Missio Germany bisa tallafi da goyon bayan da su ka bayar wajan gina gidajen da ya hada makaranta, da wuraren ibadar Kiristoci da Musulmin da zama dominsu a ka gina gidajen.
Ya ce cikin magidanta ‘yan gudun hijira 86 da’aka ginawa gidajen 14 daga ciki musulmi ne, ya ce wasu su ka taimakeshi da kudaden da ya gina masallacin ga musulmin domin su samu wajan ibada.
Haka kuma shugaban ya bada tabbacin cewa gidajen da su ke mallakin ‘yan gudun hijiran ne sun kasance da makaranta, kasantuwar babu makaranta mai inganci a yankin Unguwar Sangere Marghi, ya wadatar yaransu su samu ingantaccen ilimi.
Ya ce “mun tura yaran ‘yan gudun hijiran ingantatttun makarantu, wasu suna makarantunmu wasu kuma suna makarantun gwamnati.
“Wannan ya sa muka gina musu makaranta da wurin da gidajensu, domin yara su samu ingantaccen ilimi” Bishop Mamza.