Kwanan nan ne Karamar Ministar harkokin ‘Yansanda, Imaan Suleiman Ibrahim, ta sanar da umarnin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an ‘yansanda da ke aikin kare masu hannu da shuni a fadin tarayyar kasar nan tare da sauya musu wurin aiki nan take ba tare da bata lokaci ba.
Ta kuma bayyana cewa, a cikin umarnin a kwai shirin samar da tsarin tabbatar da tsaro a unguwanni. Mun yi murnar samar da jami’an tsaro a cikin al’umma a matsayin mataki na yaki da masu aikata laifuka a sassan kasar nan.
- Sanata Kaka Lawan Ya Gabatar Da Kudirin Tattara Dokokin Nijeriya Na Tsawon Shekara 19
- Zaben Kano: ‘Yansanda Da Masu Zanga-zanga Sun Yi Arangama A Kano
Samar da tsaro ta hanyar amfani da al’umma yana daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a tarukan jama’a na tsawon lokaci ana kuma ganinsa a matsayin wani mataki da zai kawo karshen matsalar tsaron da ake fuskanta wadda take dada karuwa a kullum musamman a yankunan karkara inda masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ke gallaza wa al’umma.
Amma kafin mu koma ga irin wannan tsarin samar da tsaron bari mu koma a kan maganar yadda jami’an tsaro ke bayar da kariya ga masu hannu da shuni a cikin al’umma, lamarin da ya munana ta yadda duk wani mai kudi a aljihunsa kuma zai iya biya sai ya nemi ‘yansanda su rika ba shi kariya.
Wani tsohon shugaban hukumar kula da aikin ‘yansanda, kuma tsohon shugaban rundunar ‘yansandan Nijeriya, Mista Mike Okiro, ya yi gargadi a kan yadda wasu ‘yan kalilan da ya kwatanta da masu hannu da shuni da kuma wasu ‘yan kadan daga cikin al’umma suke amfani da jami’an ‘yansanda fiye da 150,000 don biyan bukatun kansu.
Ya kuma ce, kasar nan ba za ta iya daukar yadda kusan rabin jami’an rundunar ‘yansanda ke aiki a hannun wasu mutane masu zaman kansu ba. Ya kuma yi korafin cewa, rundunar ‘yansanda ta kasa aiwatar da dokar janye jami’an ‘yansanda daga hidimta wa masu hannu da shuni ne saboda rashin kudi. Abin da wannan ke nufi shi ne wannan umarnin na Shugaban Kasa Tinubu na baya-bayan nan ba wai sabo ba ne, an sha bayar da irin wannan umarnin a baya amma masu amfana da al’amarin sun kasa bari a aiwatar da dokar.
Amma kuma ba wani sirri ba ne cewa, matsalar rundunar ‘yansandan Nijeriya wata aba ce da za a kwatanta da sarkakiyar kasar gaba daya. Duk da cewa, babbar matsalar da rundunar ke fuskanta ta shafi kudin gudanar da aiki amma kuma suna fuskantar karancin ma’aikata da za su taimaka musu kare al’umma yadda ya kamata, lamarin samar masu da kudi yana da muhimmaci amma shin wai rashin kudi ne matsalar ‘yansanda ko cin hanci da rashawa?.
Idan za a iya tunawa da al’amarin tsohon shugaban rundunar ‘yansada Tafa Balogun, hukumar EFCC ta tabbatar da ya sace fiye da naira Biliyan 16 cikin kudaden gudanar da rundunar.
Rundunar ‘yansandan Nijeriya a matsayinta ta daya daga cikin rundunonin tsaron kasar nan ya kamata ta bayar da muhimmanci ga rigakafin aukuwa da kuma gano masu shirin aikata laifuka ba wai su bar jami’anta na aikin kare wasu kalilan masu hannun da shuni ba a cikin al’umma.
A matsayin rundunar na hukuma mai aikin tabbatar da doka da oda, an dora wa rundunar aikin kare rayuka da dukiyiyoyin al’umma Nijeriya a duk inda suke a fadin kasar nan. Suna kuma yin haka ne ta hanyar aikawa da jami’ansu da sauran kayan aiki wurare masu muhimmanci don kare su daga ayyuykan bata gari. Haka kuma yana daga cikin ayyukan ‘yansanda samar da tsaro ga manyan ma’aikatan gwamnati da kuma manyan mutane da ke aikin gwamnati. Wannan abin da za a iya fahimta ne don wadanda ake karewa za su samu tabbacin suna da kariya a yayin da suke gudanar da aikinsu na yi wa kasa hidima.
Al’umma sun damu da ganin abin da ya kamata ya zama alfarma sai gashi an lalata shi, inda a halin yanzu jam’ai fiye da 150,000 maza da mata ke aikin kare wasu ‘yan kalilan a gidaje da ofishoshinsu na aiki, to lalai wannan ba abin da za a amince da shi ba ne.
A ra’ayijnmu ya kamata a janye ‘yansanda daga aikin ba da tsaro ga mutane da ba jami’an gwamnati ba ne, kuma da sauran masu hannun da shuni ya kamata a rage yawan jami’an ‘yansanda da ke aiki da su. A wasu lokutan sai a tura ‘yansanda fiye da biyar don gadin jami’in gwamnati daya, to lallai wannan ba abin a amince da shi ba ne.
Ba zai yiwu kasa ta yi ta fama da karancin jami’an ‘yansanda ba amma wasu da dama daga cikin jami’anta na can suna aikin kare wasu masu hannu da shuni. Don fuskantar matsalolin tsaron da ake fama da su a kasa, muna kira ga gwamnati da ta gaggauta kamma aikin daukar karin jami’an ‘yansanda a kuma tabbatar da suna yi wa kasa aiki ne ba wasu tsiraru ba.
Haka kuma wannan jaridar ta yi imani da cewa, ya kamata a tabbatar da an samar wa rundunar ‘yansanda isassun kudi da kayan aiki na zamani in har ana son su yi aiki yadda ya kamata kamar yadda ‘yansanda ke aiki a wasu kasashen duniya da suka ci gaba.