Rahotanni daga ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati a sararin samaniya na kasar Sin, sun ce da misalin karfe 1 da minti 35 na sanyin safiyar yau Jumma’a 26 ga wata, bisa hadin-gwiwar dan sama jannati Chen Dong dake cikin kumbo, sauran ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 guda biyu, wato Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da ayyuka har na tsawon sa’o’i 6 a wajen kumbon, inda suka kammala ayyukansu bisa shiri. Ya zuwa yanzu, Chen da Wang sun riga sun koma sashin gwaje-gwaje na Wentian lami lafiya, al’amarin da ya shaida babbar nasarar da suka samu wajen gudanar da ayyuka a wajen kumbon.
Yayin da suke wajen kumbon, ’yan sama jannatin biyu sun gudanar da ayyuka da dama, ciki har da saka na’urar kandagarkin tarkacen sararin samaniya a jikin tashar binciken sararin samaniya, da gudanar da bincike kan na’urorin dake wajen kumbon. Kawo yanzu, sau hudu ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 suka kammala ayyuka a wajen kumbon, al’amarin da ya sa suka zama daya daga cikin rukunonin ’yan sama jannatin kasar Sin guda biyu da suka gudanar da ayyuka mafi yawa a wajen kumbo. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp