Bayanan da aka samu a rahoto na baya-bayan nan daga Hukumar Kula da Makarantun Firamare (UBEC) yana da matukar tayar da hankali. Rahoton shekarar 2022 zuwa 2023 na kididdigar yawan Malaman firamare da ake da su ya nuna cewa, Nijeriya na fuskantar karancin malamai a matakin firamare yayin da ake da gibin Malamai fiye da Malamai 195,000 a makarantun gwamnati na fadin tarayyar kasar nan.
Karancin kwararrun Malamai a matakin farko na tsarin ilimin kasar nan abu ne da ke bukatar a dauki matakin gaggawa daga dukkan matakan gwamnati da masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan.
- Bangaren Amurka Ya Mayar Wa Bangaren Sin Da Kayayyakin Tarihi 38 Da Suka Bata Daga Sin
- Sharhi: Kokarin Fahimtar Yanayin Tattalin Arzikin Sin Ta Bangarorin Ayyuka Guda 3
Rahoton ya gano rashin daidatio a tsakanin sauran matakan ilimi, inda aka gano matakin makarantun reno na kananan yara da matakin karamar sakandare JSS suna da issasun Malamai har sun yi masu yawa amma kuma a matakin makarantun firamare suna matukar fuskantar matsalar rashin Malamai, a wasu kauyuka ma zaka ga Malami daya ne ko biyu ke aiki a dukkan makarantun da ake da su duk kuwa da yawan dalibai.
Wannan rashin daidaito na yawan Malamai a matakan ilimi na kasar nan shi ne ya jefa kasar cikin matsalolin da suke tattare da ilimin yara. Rahoton ya kuma bayyana cewa, rashin issasun Malamai a matakin firamari shi ne ya haifar matsalar talauci da sauran matsalolin da ake fuskata a Nijeriya.
A ra’ayin wannan jaridar,in har ba a samu kwararrun Malamai ba masu aiki tukuru tare da basu ingantaccen ilimi a bangaren makarantun firamare ta yaya za’a samu yara masu hazaka da za su zama abin alfaharinmu a nan gaba har su zama shugabannin gobe? Fatan kasar nan na tattare da magance wannan matsalar gaba daya.
Abin takaici a nan shi ne abubuwan da suka haifar da wannan karancin Malamai a bayyane suke kuma kowa ya san su. Yawancin jihoji sun yi shekaru basu dauki sabbin Malamai ba, yayin da wasu ma’aikata ke barin aiki wasu kuma suna mutuwa amma ba a maye gurbinsu ba.
Wannan kuma na tattare da annobar barin kasa da aka fi sani da “japa” da kwararun Malamai ke yi, hakan ya sanya Malamai masu kwazo suna barin kasarnan zuwa kasashen waje don samun rayuwa ta gari abin da kuma shine ya kara haifar da matsalar da ake ciki.
Rashin kulawa da rashin kyawun ka’idojin aiki ga Malamai a Nijeriya yana kara taimakawa wajen korar kwararrun Malamai daga bangaren suna komawa wasu wuraren inda aka san mutuncin su.
Tuni shugaban kungiyar Malamai na kasa, NUT, Kwamrade Audu Titus Amba, ya nuna rashin jin dadinsa a kan lamariin, wannan kuma yana nuna irin kamarin da al’amarin ya kai ke nan.
Ya kuma bayyana cewa, ba za a iya samun ingantacen ilimi ba har sai an samu issasun Malamai a dukkan matakai na ilimi, musamman ma ganin ilimi shi ne kashin bayan ci gaban kowadanne al’umma.
Ba wai sun kasance a matsayin Malamai kawai ba ne, su masu saita yara ne tare da shiryar da su domin su zama mutanen kirkin da za su zama shugabannin gobe.
Ba abin da za a amuince da shi ba ne a kasar da ke da yara fiye da miliyan 12 da basu zuwa makaranta duk da kuma ana fuskantar tsananin rashin Malamai a matakin firamare.
Ta yaya za mu samar da ingantaccen ilimi da kuma rage yawan yaran da basu zuwa makaranta a Nijeriya bayan kuma muna fama da matsalar karancin malamai?
Lokacin daukar matakin da bai dace ba da daukar alkawurra marasa ma’ana ya wuce yanzu lokaci ne na daukar matakin da ya dace kai tsaye.
Abin jin dadin a nan shi ne, dama can a kwai daftarin tsarin farfado da tsarin ilimi a kasar nan, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a shekarar 2020,an shirya daftarin ne don bunkasa tare da inganta sana’ar koyarwa a Nijeriya.
Wannan ya hada da samar da albashi na musamman ga Malaman firamare da na sakandare tare da kara shekarun barin aikin su hakanan kuma an samar da alawus alawsu ga dalibai masu koyon aikin Malanta don karfafa masu shiga harkar koyarwar.
Abin takaici a na shi ne irin wannan kyawawan matakai da kudurori ba a kai ga aiwatar da su ba har zuwa yanzu wanda hakan ke ci gaba da sanya harkar koyarwa cikin halin ni ‘yasu.
Dole ne a gaggauta daukar mataki kan wannan lamarin da gaggawa, sai aiwatar da abin da ke tatatare cikin shi rahoton.Muna kira da wannan gwammantin a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince da daukar muhimmin mataki wajen aiwatar da tsare-tsaren da tsohon shugaban kasa Buhari ya yi na farfado da bangaren ilimi.
Bayan haka kuma dole gwamnatocin jihohi su dauki nasu alhakin.Dole su gaggauta fara daukar sabbin Malamai don cike gurbin Malaman firamare da aka rasa musamman a yankunan karkara.
Ya kuma kamata a kara inganta ka’idar aiki da jin dadin Malamai don aikin ya zama yana da ban sha’awa ta yadda kwarrarun Malamai za su tsaya a cikin aikin ba tare da shirin tserewa zuwa kasashen waje ba.
Lokaci ya yi da gwamnati tare da hadin gwiwar dukakan masu ruwa da tsaki su dauki matakin ganin kowanne yaro a Nijeriya ya samu damar zuwa makarannta tare da samun ilimin da ya kamata.
Nasarar yaran Nijeriya dama nasarar Nijeriyar tana tattare ne da nasarar da aka samu a wannan kokarin. In muka zuba jarin da ya kamata a bangaren ilimi za mu samar da yaran da za mu yi alfahari da su a nan gaba.