Sabon zakaran da babu kamar sa a duniya a fannin kwallon kafa, Karim Benzema, ya bayyana cewa bashi da burin komawa wata kungiyar domin ya buga mata wasa kuma a Real Madrid yake fatan ajiye takalmansa.
A ranar Litinin ne dan wasan na Real Madrid, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d’Or bayan ya ci kwallo 44 a wasanni 46, wanda ya bayar da gudunmuwar da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League a kaka wasa ta 2021 zuwa 2022.
Dan wasan PSG Lionel Messi mai rike da kyautar bara mai bakwai jumulla da Cristiano Ronaldo mai biyar, sun lashe 12 daga Ballon d’Or 13 baya kuma shekara 17 akayi ana yin wannan bikin da Messi.
‘Yar wasan Barcelona, Aledia Putellas ce ta sake lashe gwarzuwar kwallon kafa ta duniya ta 2022 sannan ‘yar kwallon Ingila da ta ci Euro 22 mai buga wasa a Arsenal, Beth Mead ce tazo ta biyu.
Manchester City, wadda take da ‘yan takara shida ta lashe kyautar kungiyar da babu kamarta kuma sannan an bayar da kyautar bana bisa kwazon dan wasa a kakar wasa ta 2021 zuwa 2022, maimakon shekara daya da ake yi a baya.
Benzema shi ne dan kasar Faransa na farko da ya lashe Ballon d’Or tun bayan 1998 kuma Zidane ne ya lashe kyautar a shekarar 1998, kuma shi ne ya bai wa Benzema kyautar a bikin na bana.
Jerin Mutum 20 dake kan gaba a iya kwallo a duniya
1. Karim Benzema (Real Madrid, France).
2. Sadio Mane (Bayern Munich, Senegal).
3. Kevin de Bruyne (Manchester City, Belgium).
4. Robert Lewandowski (Barcelona, Poland).
5. Mohamed Salah (Liverpool, Egypt).
6. Kylian Mbappe (Paris St-Germain, France).
7. Thibaut Courtois (Real Madrid, Belgium).
8. Vinicius Junior (Real Madrid, Brazil).
9. Luka Modric (Real Madrid, Croatia).
10. Erling Haaland (Manchester City, Norway).
11. Son Heung-min (Tottenham Hotspur, South Korea)
12. Riyad Mahrez (Manchester City, Algeria).
13. Sebastien Haller (Borussia Dortmund, Ivory Coast).
14. Fabinho (Liverpool, Brazil) tied with Rafael Leao (AC Milan, Portugal).
16. Birgil ban Dijk (Liberpool, Netherlands).
17. Luis Diaz (Liverpool, Colombia) tied with Dusan Blahobic (Juventus, Serbia) and Casemiro (Manchester United, Brazil).
20. Cristiano Ronaldo (Manchester United, Portugal).