Kiran da ‘yan Nijeriya suka dade suna yi na neman a sake fasalin Rundunar ‘Yansanda kasar nan a halin yanzu ya zama wani lamari da ke bukatar a dauka da muhimmancin gaske. ‘Yan Nijeriya da dama sun yi ittifakin cewa, in har ana son Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ta yi aikin kare al’umma da dukiyoyinsu yadda ya kamata dole a kakkabe duk wani burbushin mulkin mallaka da na sojoji da ke tattare da yadda suke gudanar da ayyukansu. Wadannan dabi’u ne suka sa ake yawan zarginsu da rashin iya aiki, cin hanci da kuma gallaza wa al’umma. A Nijeriya kamar sauran kasashe, an samar da rundunar ‘yansanda ne don kare al’umma tare da tabbatar da doka da oda amma ba wai don takura wa al’umma ba.
An dai fara samar da jami’an tsaron ‘yasanda a kasar nan ne a shekarar 1820, a zamanin mulkin mallaka, ta kuma fuskanci sauye-sauye da dama tun daga lokacin da aka kafa ta, amma kuma rundunar ta kasa tafiya daidai da zamani, ana kuma ganin yadda take gudanar da ayyukanta ba su dace da zamani ba. A kan haka ne, babu tantama in aka ce Rundunar ‘Yansandan Nijeriya na tsananin bukatar sauyin fasali don magance matsalolin da take fuskanta a kokarinta na karfafa wa al’umma gwiwa da kuma kokarinta na tabbatar da doka da oka a fadin tarayyar Nijeriya.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Kira A Kwantar Da Hankali Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
- Akwai Kyakkyawan Fata Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka A Wannan Karo
An sha yin kokarin ganin an sake fasalin rundunar a baya, amma al’amarin bai kai ga samun nasarar da ake bukata ba. Kokari na baya-bayan nan an yi shi ne bayan tarzomar da ta biyo bayan zanzangar #EndSARS da aka yi a watan Oktoba na shekarar 2020, yadda aka sake fasalin bai samar da sauyin da ake bukata ba, don bai yi maganin manyan matsalolin da ake fuskanta ba. A kan haka ne muke maraba da sabbin ‘yan kwamitin shugaban kasa a kan sauya fasalin Rundunar ‘Yansanda da aka kaddamar.
Kwamitin da ya hada da Ministan Harkokin ‘Yansanda, Ibrahim Geidam, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaron kasa, Nuhu Ribadu, Shugaban Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda, Solomon Arase da shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, an nemi su hada kai tare da samar da hanyoyin yi wa rundunar garambawul. Muna fatan a wannan karon gwamnati za ta gano bakin zaren warware matsalar yadda ya kamata.
A ra’ayinmu babban kalubalen da ke fuskantar Rundunar ‘Yansandan shi ne cin hanci da rashawa. Al’umma na ci gaba da kyamar ‘yansanda saboda yadda suka baci da cin hanci da rashawa a yayin gudanar da harkokinsu. Wannan ya haifar da rashin aminci a tsakanin ‘yansanda da al’umma, hakan na faruwa ne saboda ‘Yan Nijeriya na ganin kamar ‘yansanda sun fi damuwa ne da batun kudi a kan aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Sakamakon wannan rashin aminci ne sau da dama al’umma ba su bayar da rahoton aikata laifuka a yankin da suke, saboda mutane na ganin babu wani amfani a taimakon ‘yansanda.
Wani kalubalen da rundunar ‘yansandan ke fuskanta shi ne na yadda suka zama masu muzgunawa. An dade ana zargin ‘yansandan da amfani da karfin da ya wuce kima wajen gallaza wa ‘yan Nijeriya wanda yakan kai ga jin ciwo ko kuma mutuwa a wasu lokuta. Wannan yakan kai ga zanga-zangar neman a yi wa wanda aka kashe adalci amma sau da dama ba a yin komai don magance lamarin. An sha samun jami’an ‘yansanda sun kashe mutum amma babu wani mataki da ake dauka a kan jami’in da ya yi kisan.
Amma kuma muna tausaya wa ‘yansanda saboda za ka samu ba su da kayan aiki na zamai ba su kuma da horo na musamman na yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. ‘Yansanda da dama ba su da muhimman kayan aiki da suka hada da bindigogi, rigunan sulke da motocin sintiri. Wasu ma daga dan abin da ake ba su na albashi suke saya wa kansu tufafin aiki (uniform). Wannan na kawo musu cikas a yayin da aka nemi su kawo dauki na gaggawa don kare al’umma.
In har ana son ‘yansanda su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, dole sauyin fasalin da za a yi ya mayar da hankali wajen kawar da cin hanci da rashawa, kawo karshe cin zarafin al’umma da kuma magance rashin isassun kayan aiki a tsakanin ‘Yansandan Nijeriya, a kuma dawo da yarda da aminci a tsakaninsu da al’umma. Ya kuma kamata a samar musu da albashin da zai sa su kawar da kai daga karbar na goro daga al’umma, irin wanna ne yakan sa su nemi huce haushinsu a kan al’umma da zarar wani dan abu ya hada mutane da su.
Hanyar magance matsalar ita ce, dole gwamnati ta zuba jari wajen horas da jami’an ‘yansanda tare da samar musu da kayan aiki na zamani irin wanda ‘yansandan wasu manyan kasashen duniya ke amfani da su.
A bangaren ‘yansandan kuma, ya kamata a tabbatar da hukunta duk wani jami’n da aka samu da karbar cin hanci ko kuma wadanda suka ci zarafin mutane, a hukunta su kamar yadda doka ta tanada, wannan zai karfafa zuciyar al’umma ya kuma dawo da aminci a tsakanninsu da ‘yansandan.