Kwanakin baya shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Maiduguri, Malam Umar Habeeb Jibril, ya bayyana cewa, dalibai 2 ne daga cikin dalibai 89 da suka samu gurbin karatu a kwalejin suka yi rajista, sauran sun kaurace saboda karin kudin makaranta da aka yi. Makarantar da ya kamata a ce ta dauki dalibai 200 amma sai ta dauki 89 kuma daga cikinsu mutum biyu ne suka zo don yin rajista, a matsayin sabbin dalibai.
Shawarar gwamnatin tarayya na kara kudin makaranta daga Naira 45,000 zuwa Naira 100,000 ya sa dole iyaye suka janye yaransu daga makarantun saboda yadda suke fuskantar radadin matsalar tattalin arziki wanda da al’umma ke fuskanta a fadin kasar nan a halin yanzu.
- Zamu Sabanta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
- Sin Ta Yi Kira Da A Hada Kai Wajen Samar Da Tsaron Fasahar AIÂ
Wannan lamarin a ra’ayinmu zai kara ta’azzara matsalar da ake fuskanta a makaratunmu na rashin yara masu zuwa makaranta, zai kuma kara yawan yara masu gararamba a titunan kasar nan ba tare da zuwa makaranta ba.
Kididdiga daga Hukumar Kula da Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta nuna cewa akwai fiye da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.
A kan haka ne, yana da wahalar gaske a iya fahimtar dalilin da ya sa gwamnati ta kara kudin makaranta da kuma yekuwar da take yi na rage yara da ke gararamba a tituna ba sa zuwa makaranta. Wannan shawarar karin kudin makaranta, mataki ne na hana iyaye daga tura yaransu makaranta, musamman ma talakawa da masu gwagwarmayar neman yadda za su samu abin kaiwa bakin salati, abin takaicin ma shi ne makaratun gwamnati sun fi karfin ‘yan Nijeriya talakawa ballantana makarantu masu zaman kansu.
Wani karin abin takaici a nan shi ne, a yankin arewa maso gabas, wanda ya hada da Jihar Yobe, Taraba, Bauchi, Gombe Adamawa da Borno, an kiyasta cewa, kashi 33 cikin 100 na yaran yankin ba sa zuwa makaranta, wanna shi ne mafi yawa a kasar gaba daya, a yankin arewa ta tsakiya kuma akwai kashi 26, Arewa ta yamma akwai kashi 25; kudu maso kudu kuma kashi 24; kudu maso yamma kashi 22 yayin da kuma kudu maso gabas ake da yara kashi 19 da ba sa zuwa makaranta.
Da yawa daga cikin wadannan ‘ya’ya suna gararamba a kan titunan kasar nan inda daga karshe suna zama ‘yan bangar siyasa, wani abin tashin hankali kuma shi ne yadda wasu yaran ke zama abin da wasu bata gari ke amfani da su wajen gudanar da tsaface-tsaface ko kuma su zama makamin da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen aikata ayyukansu na tarzoma a kasa.
Babu tantama, shawarar gwamnati ta kara kudin makaranta a daidai wannan lokacin da ake fuskantar matsalar tattalin arziki ce ta tilasta wa wasu gidaje rage abincin da suke ci a rana, wanda kuma wannan a ra’ayinmu yana nuna yadda gwamnati ba ta dauki harkar ilimi da muhimmancin da ya kamata ba.
Bayanin da ya fito daga shugaban makaranta, Jibril, ya fayyace laifin gwamnatin tarayya karara wadda ya kamata a ce tana kokarin ganin tana karfafa matakin rage yaran da ba su zuwa makaranta a fadin kasar, yana kuma nuna cewa, gwamnati ba da gaske take yi ba na cimma manufofin da suka sa aka kafa makarantun tun da farko.
Idan za a iya tunawa an kafa makarantun hadin kan kasa ‘Unity School’ ne don samar da wani dandamali da zai hada kan ‘yan kasa da kuma gina kasa, an kuma tabbatar da za a iya cimma wannan burin ne ta hanyar samar wa da yara yanayin da za su zauna a wuri daya, su yi karatu a wuri daya, ta yadda hakan zai samar da fahimtar juna a tsakaninsu.
Yana kuma da muhimmanci a fahimmaci cewa, an kafa kwalejojin gwamnatin tarayya na farko ne a shekarar 1964 a a garuruwan Sakkwato (Arewa); Okposi (yankin Kudancin kasar nan) da kuma Warri a yankiin kudu ta tsakiya.
Daga baya aka kafa wasu makarantun don cika burin gwamnatin tarayya na hada kan kasa. Amma kuma abin takaici, a ‘yan shekaru nan aka bar makarantun suka lalace saboda rashin kudaden gudanarwa da kuma rashin sa ido daga bangaren gwamnati.
Kafin ma a yi wannan karin kudin makarantar wanda a halin yanzu ya sa makarantar ta fi karfin talaka, an dade ana tunanin yadda gawmnati ta yi sako-sako da kudurinta na daukar nauyin gudanar da makarantun saboda yadda aka fuskanci karancin kudin gudanarwa da kuma sa ido daga gwamnatin.
Kamar dai sauran ‘Yan Nijeriya, mun damu da rahoton da ke fitowa daga kwalejin gwamnati na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, cibiyar kungiyar Boko Haram da ake kyamar karatun boko.
Ya kamata gwamnati ta dauki matakin gaggwa na rage kudin makarantaun kwalejin gwamnatin tarayya don a samu karin yara masu shiga makarantar musamman ganin yadda ake kokarin cike gibin yaran da ba su zuwa makaranta. Babu wani dalilin yin wannan karin, musamman ganin yadda karin ya haifar da raguwar yara masu shiga makaranta a daidai lokacin da gwamnatin ke so a samu karin yara masu zuwa makaranta, ya zama dole a sake shawara.
Abin takaici ne a ce an bullo da wata manufar gwamnati da ta hana yara zuwa makaranta, musamman a yankin da ‘yan ta’adda ke takura al’umma daga shiga makarantun boko kuma ake da yara masu yawa da ba su zuwa makaranta.
Ra’ayinmu a nan shi ne, ya kamata a ce gwamnatoci a dukkan matakai su dauki nauyin karfafa hanyoyi shigar da yara makaranta da tabbatar da suna ci gaba da karatun tare da kammala karatun a matakin firamare, sakandire kamar dai yadda dokar bayar da ilimi kyauta ta tanada a kundin tsarin mulkin kasar nan.