• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abba Gida-Gida Bai Cancanci Zama Gwamnan Kano Ba –APC

by Sadiq
3 years ago
APC

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta shigar da kara a gaban kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano da ke zamanta a Miller road, tana kalubalantar nasarar zababben gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an shigar da karar ne a gaban kotun ta hanyar rajista, a ranar 9 ga Afrilu, 2023.

  • Mutum 17 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Garkuwa Da Mutane A Ekiti
  • NIS Ta Kaddamar Da Shirin ‘Guguwa’ Don Dakile Kwararar ‘Yan Ci-Rani A Ribas

APC ta sanar da kotun cewa sunan zababben gwamnan jihar, Abba Kabiru Yusuf baya cikin jerin rajistar NNPP da ke hannun INEC.

APC ta bayyana a cikin karar cewa kafin zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023, dan takarar jam’iyyar NNPP ya gaza cika sharuddan zama mamba jam’iyyar, don haka ake zargin bai cancanci tsayawa takara a zaben gwamna a karkashin jam’iyyar NNPP ba.

Bugu da kari mai shigar da kara suna rokon kotu da ta rusa wa’adin zaben Abba.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

APC ta bukaci kotun da ta amince da adadin kuri’un da aka kada ba bisa ka’ida ba, don haka a yi la’akari da yadda aka cire adadin kuri’un da aka soke ba bisa ka’ida ba tare da ayyana zaben a matsayin ‘Inconclusive’.

Masu gabatar da kara, sun bukaci NNPP da dan takararta na gwamna da INEC wa’adin kwanaki 21 don amsa batutuwan da masu shigar da kara a kai.

A wani lamari makamancin haka, kotun ta bai wa jam’iyyar APC takardar bukatar duba kayan zaben gwamna, a wani bangare na ci gaba da shari’ar su da NNPP a gaban kotu.

Mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar APC Jihar Kano, Abdul Adamu Fagge, ya tabbatar da cewa tawagar jam’iyyar APC ta fara duba kayayyakin zaben da aka yi amfani a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

A cewarsa aikin duba kayayyakin yana gudana cikin kwanciyar hankali tare da goyon bayan dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa babu wata tangarda da ake sa ran za ta kawo cikas ga aikin, inda ya ce an ba su damar yin amfani da dukkan kayan ya zuwa yanzu, inda ya ce jam’iyyar za ta bibiyi lamarin har zuwa ga doka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
Manyan Labarai

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara
Manyan Labarai

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025
Next Post
Xi Jinping: Akwai Makoma Mai Haske A Fannin Raya Sana’o’i Na Musamman A Yankunan Karkara

Xi Jinping: Akwai Makoma Mai Haske A Fannin Raya Sana’o’i Na Musamman A Yankunan Karkara

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.