Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, ya ce zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na son fara shugabancin jihar da kuskure.
Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, na jam’iyyar NNPP, ya kasance suna jifan juna shi da Ganduje kan filaye da gine-ginen gwamnati.
- Firaministan Kwadibuwa Na Sa Ran Za A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Kasarsa Da Sin
- Saudiyya Ta Damke Bakin Haure Sama Da 16,000
Ganduje ya gargadi Abba Gida-Gida cewa har yanzu shi ne ke rike da ragamar mulkin jihar kuma yana da kyau ya jira har sai an rantsar da shi a matsayin gwamna.
A yayin da yake zantawa da manema labarai bayan addu’ar da aka shirya wa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a gidan gwamnati da ke Kano, gwamnan mai ci ya bayyana cewa gwamna mai jiran gado ya nuna cewa shugabancinsa ba shi da alkibla.
A cewar Ganduje, “Wannan alama ce ta nuna cewa shugabancinsu ba shi da alkibla domin irin wannan shawara ba ta da tushe.”
Ya bayyana cewa zababben gwamnan yana magana kamar yanzu shi ne gwamnan Jihar Kano, yana mai cewa har yanzu bai zama gwamna ba kuma yana addu’ar ya yi mulki lafiya.
Ya koka da yadda zababben gwamnan ya fara shawartar masu gine-gine a filayen gwamnati da su dakata, yana mai cewa mutum zai iya yin hukunci idan ya karbi ragamar shugabanci.
Zababben gwamnan ya do ke mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Da farko Gawuna ya ki amincewa da nasarar Yusuf, amma daga baya ya yi wa Abba Gida-Gida fatan nasara.