Hukumomin Saudiyya sun ce sun kama bakin haure 16,407 da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba, a yankuna daban-daban cikin mako daya.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar na cewa an kama mutanen ne bayan wani samamen hadin gwiwa da jami’an tsaro suka kaddamar a sassa daban-daban cikin wannan wata na Ramadan.
Kamen ya hadar da mutunen da suke zaune a kasar ba tare da izini ba, da mutunen da ba su da takardun shiga kasar, sai kuma mutunen da suka saba ka’idojin aiki na Saudiyya.
Ma’aikatar ta ce ta kama wasu a lokacin da suke kokarin tsallaka kan iyakar kasar, wasu kuma an kama su ne lokacin da suke yunkurin fita daga kasar.
Ta ce kashi 74 na waÉ—anda aka kama, ‘yan Habasha ne, sai kashi 22 ‘yan asalin Yemen, kashi hudu kuma na sauran kasashe.
Ma’aikatar cikin gidan ta ce an tura ‘yan ci-rani 6,251 zuwa ofisoshin jakadancin kasashensu da ke Saudiyya don samar musu takardun izini, yayin da za a mayar da mutum 10,156 zuwa kasashen da suka fito.
Ta dai gargadi duk wani mutum da ya yi sanadin shigar da wani bakon haure cikin Saudiyya ba bisa ka’ida ba, ko ya ba shi masauki, ko aiki, da dai duk wani nau’in taimako – ya tabbatar cewa zai fukanci hukuncin da zai iya kai wa daurin shekara 15 a gidan yari, matukar aka kama shi.
Sannan da biyan tarar riyal miliyan daya, idan aka same shi da laifin hada baki wajen shigar da bakin haure cikin kasar, da kuma samar musu masauki.