• English
  • Business News
Tuesday, July 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan

by Muhammad
3 weeks ago
in Tattaunawa, Siyasa
0
Gwamnan Abba Kabir Yusuf tare da Arch. Ali Hassan

Gwamnan Abba Kabir Yusuf tare da Arch. Ali Hassan

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Arch. Ali Hassan, matashin ɗan kasuwa ne kuma ƙwararren mai tsara taswirar gine-gine na zamani, an haife shi a Kano, ya kuma girma a Kano. Ya yi karatu kan gine-gine da tsara birane a ƙasar Italiya, mutum ne mai kishin ƙasa da ƙwarewa kan harkokin zamani. A cikin wata tattaunawa da ya yi da wakilin Jaridar LEADERSHIP HAUSA ya bayyana irin sauyin da jihar Kano ke samu cikin hanzari a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, a yayin cikarsa shekaru biyu akan mulki a matsayin gwamnan Kano.

A matsayinka na ɗan asalin Kano kuma ƙwararren mai ilimin kan gine-gine daga ƙasashen waje, yaya kake ganin halin da Kano ke ciki a yau a ƙarƙashin wannan gwamnati?

Abun farin ciki ne a gare ni na samu damar tattauna wani abu da ke da matuƙar muhimmanci a zuciyata, wato Kano. Na taso a nan Kano, amma na yi karatu a Italiya, inda na samu ilimi kan harkokin tsara birane da gine-gine na zamani da bunƙasa su. Da na dawo gida kuma na ga abubuwan da ke faruwa yanzu a ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, sai na ce wannan sabon yunƙuri ne na ci gaba sosai. A cikin shekaru biyu kacal, gwamnan ya sauya Kano da fasalinta gaba ɗaya. Tun daga al’amuran da suka shafi ababen more rayuwa zuwa bunƙasa harkokin jama’a, da farfaɗo da tattalin arziƙi da zaman lafiya ta yadda Kano ta shiga jerin manyan birane ba kawai a suna ba kaɗai, har ma a zahiri.

  • Ƴansanda Sun Gargaɗi Masu Lalata Fastar Tinubu A Kano
  • Bam Ya Fashe A Kano, Ya Kashe Mutane 5

Ka ce Kano ta shiga taswirar manyan birane a duniya, me kake nufi da hakan?

Na faɗi haka ne saboda a matsayina na wanda ya rayu kuma ya yi karantu a ƙasashen waje, na shaida yadda manyan birane ke haɓaka. Kuma makamancin haka yanzu na ke gani a Kano. Akwai ayyuka masu yawa na gina sabbin tituna da gyare-gyaren birni, da kuma inganta kyawun gari. Kasuwanni ana sake tsara su, masana’antu suna dawowa, kuma batun samar da ayyukan yi ya wuce alkawari kawai da fatar baki, ya zama a gaske. A ɓangaren walwalar al’umma kuma, an inganta harkokin kiwon lafiya da makarantun gwamnati da ba su kulawa, kuma kowa yana jin cewa yana da muhimmanci a cikin al’umma. Waɗannan su ne abubuwan da ke gina babban birni, wanda Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ke gina wa da samarwa a Kano.

Labarai Masu Nasaba

Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna

Tun da ka yi karatu a Italiya, yaya kake kwatanta ci gaban Kano, da na wasu biranen zamani da ka sani?

Wannan tambaya ce mai amfani. Birane irin su Milan da Florence da Turin, suna da dogon tarihi a fannin ci gaban birane amma abin da ke bambanta Kano a yanzu shi ne saurin aiki da kuma hangen nesa, kuma wannan gwamnati tana da tsari a fagen. A matsayina na mai tsara gine-gine, zan iya saurin gano kyakkyawan shiri idan na gan shi. Kuma abin da ke faruwa a Kano ya na da kyau sosai. Ana gabatar da abubuwa masu alaƙa da biranen zamani, wato wuraren shakatawa da sanya fitilun titi da magudanan ruwa da kuma kula da tsarin taswirar gine-gine. Haƙiƙa wannan wata alama ce da take nuna gwamnati ta ƙuduri kawo ci gaba a zahiri.

Wasu suna cewa shekaru biyu ba su isa a auna nasarar gwamnati ba. Mene ne ra’ayinka gane da hakan?

A wannan magana, ban yarda da ita ba. Shekaru biyu ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf, sun haifar da abubuwan da wasu shugabanni ba su iya yi ba a cikin shekaru takwas da suka yi suna mulki ba. Duk abinda aka gina kan tubali nagari, ba sai an jira dogon lokaci ba za a fara ganin tasirinsa, abin da kawai ake buƙata shi ne jagoranci nagari. Kuma hakan muna da shi a yanzu. Ayyukan da ya yi cikin shekaru biyu ya cancanci a rubuta su cikin tarihi.

Wasu na cewa irin waɗannan shugabanni su na da buƙatar a ba su dama su ci gaba da mulki fiye da iyakar wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada. Me za ka ce akan haka?

Wannan gaɓa ce mai mahimmanci, wanda lokaci ya yi da ya kamata mu sauya yadda muke kallon shugabanci. Idan muna da shugaba mai hangen nesa da bayar da sakamako, kuma wanda ke tafiyar da mulki kan buƙatun al’umma kamar Injiniya Abba Kabir Yusuf, me zai hana a ɗora da ci gaban da yake kawo wa? Da alama kamar muna hukunta nasara ne idan muka taƙaita irin wannan shugaba zuwa wa’adi biyu wato “4+4”. Irin waɗannan shugabanni misali ne ba kawai ga Nijeriya ba, har ma ga nahiyar Afirka da duniya baki ɗaya. Idan akwai buƙatar sauya tsarin mulki don bayar da damar ci gaba da irin wannan jagoranci, to ya dace mu fara tattaunawa a kan haka, don ci gaba bai kamata a katse shi ba saboda al’ada.

A ƙarshe wane saƙo za ka bai wa jama’ar Kano da matasa ‘yan kasuwa irinka?

Ga jama’ar Kano, wannan lokacinmu ne da za mu tallafa wa wannan jagoranci mai hangen nesa ta hanyar bayar da gudummawa wajen ɗaukar nauyin ci gaban da ke faruwa a garuruwan mu. Ga matasa ‘yan kasuwa kuma ku duba Kano yanzu. Dama tana bayyana a ɓangarori daban-daban daga gine-gine, da fasahar zamani (IT), da masana’antu, har ma da yawon buɗe ido. Lokaci ne da ya dace mu fara tunani mai zurfi, tare da shirin ƙara jajircewa don bayar da gudummawa wajen gina sabuwar Kano.

Gwamna na cika shekaru biyu a mulki, mene ne saƙonka na ƙarshe?

A ƙarshe, ina mika gaisuwa ta musamman ga mai girma gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa cikarsa shekaru biyu kan karagar shugabanci nagari. Haƙiƙa ya nuna mana yadda salon jagoranci nagari ya ke, tare da yadda ake fifita muradun jama’a a tsarin shugabanci, muna miƙa saƙon gaisuwa tare da nuna alfahari da shi.

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf tare da Arch. Ali Hassan suna gaisawa yayin wani taro a fadar gwamnatin Kano.
Gwamnan Kano, Abba K. Yusuf tare da Arch. Ali Hassan yayin wani taro a fadar gwamnatin Kano.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abba Gida-gidaAbba Kabir YusufArch. Ali HassankanoTsara Birane
ShareTweetSendShare
Previous Post

2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega

Next Post

Hajji 2025: Kashi Na Farko Na Alhazan Abuja Sun Dawo Gida Nijeriya

Related

Ko Yanzu Tinubu Ya Yi Rawar Gani, Kuma Yana Ƙoƙari Sosai – Buhari
Rahotonni

Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari

1 day ago
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Labarai

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna

4 days ago
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
Manyan Labarai

Shugabannin Jam’iyyar ADC Na Jihohi 36 Da Abuja Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga David Mark

4 days ago
Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta
Labarai

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

4 days ago
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe
Siyasa

Babu Wanda Ya Buƙaci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC

6 days ago
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027

7 days ago
Next Post
Hajji 2025: Kashi Na Farko Na Alhazan Abuja Sun Dawo Gida Nijeriya

Hajji 2025: Kashi Na Farko Na Alhazan Abuja Sun Dawo Gida Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha 

Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha 

July 14, 2025
Dangote Na Neman Izinin Gina Babbar Tashar Jiragen Ruwa Mafi Zurfi A Nijeriya

Dangote Na Neman Izinin Gina Babbar Tashar Jiragen Ruwa Mafi Zurfi A Nijeriya

July 14, 2025
Sin Da Amurka Na Kokarin Tabbatar Da Ci Gaban Da Aka Samu Na Yarjejeniyar London

Sin Da Amurka Na Kokarin Tabbatar Da Ci Gaban Da Aka Samu Na Yarjejeniyar London

July 14, 2025
Sarkin Maroko Ya Aike Da Ta’aziyya Ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari

Sarkin Maroko Ya Aike Da Ta’aziyya Ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari

July 14, 2025
Sin Na Maraba Da ’Yan Jaridar Duniya Da Su Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Harin Japan Da Na Tafarkin Murdiya 

Sin Na Maraba Da ’Yan Jaridar Duniya Da Su Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Harin Japan Da Na Tafarkin Murdiya 

July 14, 2025
Osimhen Na Dab Da Komawa Galatasaray Na Dindindin

Osimhen Na Dab Da Komawa Galatasaray Na Dindindin

July 14, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

July 14, 2025
Za A Iya Yarda Da Buhari Kan Kowace Irin Amana A Duniya — Abdulsalami

Za A Iya Yarda Da Buhari Kan Kowace Irin Amana A Duniya — Abdulsalami

July 14, 2025
Cinikayyar Shige Da Fice Ta Sin Ta Karu Da Kaso 2.9 Bisa Dari A Watanni Shida Na Farkon Bana

Cinikayyar Shige Da Fice Ta Sin Ta Karu Da Kaso 2.9 Bisa Dari A Watanni Shida Na Farkon Bana

July 14, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 1,111, Sun Yi Garkuwa Da 276 A Nijeriya Cikin Watan Yuni

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 1,111, Sun Yi Garkuwa Da 276 A Nijeriya Cikin Watan Yuni

July 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.