Connect with us

LABARAI

Abdulsamad Isiyaka Ya Bada Tallafin Naira Biliyan Uku Ga Kano

Published

on

Kasaitaccen attajirin nan dan asalin Jihar Kano, Alhaji Abdulsamad Isiyaka Rabiu, ya bayar da tallafin Naira biliyan 3.3 a jihar, don taimaka wa yunkurin da a ke yi na yaki da annobar cutar Korona.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun attajirin da kansa ta hannun gidauniyar kamfaninsa na BUA Foundation a jiya Lahadi, 26 ga Afrilu, 2020.

Ya ce, ya bayar da gudunmawar ne, domin ganin yadda annobar cutar ke kara yin tsamari, musamman ma a Kano da Legas.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: