Mamallakin Jaridar ‘Daliy Nigerian’ wanda ya fallasa faifan bidiyon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na Dala ya bayyana yadda suka gana da gwamnan a Landan.
Dan jaridar dai ya yi hijira tun a shekarar da wuce kan zargin cewar ana farautar rayuwarsa.
- An Fitar Da Rahoton Masana Kan Ra’ayin Kare Hakkin Dan Adam Na Sin
- PDP Ta Yi Tir Da Barazanar Da Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu Yake Yi wa Kafafen Yada Labarai
“Wato gamo muka yi, wanda shi ya je a matsayinsa na daya daga cikin tawagar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu ni kuma na je a matsayina na dan jarida wajen da ake gudanar da taruka wanda shugabanni na kasashen duniya su kan zo.
“Bayan an fito daga taro sai muka hada ido sai muka cafke muka yi raha aka tafi, ba dai wani aby da aka yi.
“Na zolaye na ce ranka ya dade kwana biyu, ya ce Ja’afar ka gudo, na ce kai ka koro ni, ya ce ba shi ya koro ni ba; irin dai wadannan maganganun na raha ba wai wasu maganganu aka yi na abin nan ba.
“Duka-duka tsayawar tamu da muka yi ba ta wuce minti daya zuwa biyu ba, amma ba wani abu da aka ce gaskiya, har yanzu dai a nan a matsayin da ake.
“Kuma a matsayinmu na Musulmai tun da shugaba ne tun da ba doke-doke kuke yi ba, tun da an kai munzalin da ba wani ne zai doki wani ba, dole idan an hadu a yi musabiha,” in ji shi.
Faifan bidiyon da Ja’afar Ja’afar ya saki kan Ganduje yana sanya Dalar Amurka a aljihun babbar rigarsa ya hargitsa siyasar Kano, lamarin da ya sanya majalisar dokokin jihar aike wa dan jaridar sammacin bayyana a gabanta don kare ingancin bidiyon da ya yada a kafarsa.
Tun daga wannan lokaci aka shiga yi wa gwamnan na Kano shagube da kalmar ‘Gandollar’.