Shuaibu Aliyu Mai Yasin" />

Abin Da Ya Kamata Mutum Ya Yi Ranar Zabe

Idan ‘yan Nijeriya sun lura za su gane cewa, Allah Subhanahu Wata’ala ya san dalilin da ya sa ya yi mu a ‘yan Nijeriya. Ma’ana bai yi mu a cikin mutanen Indiya ba, kuma mu ba mutanen kuma ba mutanen Ghana ba, to Ashe ya kamata mu gane cewa, babu wata kasa wadda in ta lalace to mu ne muka lalace sai Nijeriya, kuma sai ta inganta sa’ilin nan mu ma mu samu inganci kodayake mu ne ya kama mu inganta ta, ta hanyar zaba mata shugaba ingantacce.
Ra’ayoyi sun bambanta a kan cewa, Buhari ne ko Atiku ne? wanne ya fi cancanta, to gaskiya dukkaninsu sun cancata sai dai kawai wanda ka fi so to shi ya fi cancata a wurinka. Amma idan an bai wa addinin Musulinci dama za mu gane da cewa shi fa wanda ake yi wa shaidar ba ya sata ko bai taba sata ba to babu wani mahaluki da zai iya bada shaidar cewa Shaidan ba zairinjaye shi da yin satar ba, haka nan shi ma wanda ake yi wa shaidar cewa yana sata ko ya yi sata shi ma babu wani mahaluki da zai iya bada shaidar cewa Allah ba zai shirye shi ba.
Sai a wayi gari ya zama dan kasa nagari, domin ita dai shiriya ta Allah Subhanahu Wata’ala ce. Ya kuma gaya wa Manzonsa (S.A.W) cewa “innaka latahdi man ahbabta walakinnalaha yahdi manyasha’u min ibadihi”
To kai da kake da gwani ya yakama ka yi? shin zagi da batanci ga wadanda ba ka ra’ayi musamma ga shugabannin kasarka da kake wa fatan alheri. Kar dai mu manta Allah Subhanahu Wata’a’la yana cewa, “Mayalfazu minkaulin illa ladaihi Rakibun Atidun”.
To ashe fadin alheri ga mutane ya fi zama salama gobe kiyama, shi kuma fadin sharri ga mutane yakan zama nadama gobe kiyama, sanna kuma ga shi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Man kana Yuminu Billahi Walyaumul Akhiri Falyakul Khairan Au Liyasmut” Buhari da Muslim suka ruwaito.
To zagi da batanci ga mutane Nijeriya ba zai zame wa Nijeriya alkairi ba, ashe kuma ba abin mamaki ba ne in kun shagala da zagin ‘yan uwanku ‘yan Nijeriya sai mutanen Indiya su yi muku dariya kuma mutanen Ghana su gane da cewa ku dai ba ku gane ba, domin son wanda kake so fa ba zai sa Allah Subhanahu Wata’ala ya ba shi mulki ba.
Haka nan kuma kin wanda kake ki da zai hana Allah Subhanahu Wata’ala ya ba shi mulki ba musamman idan mun lura da cewa Subhanahu Wata’ala yana cewa shi dai ne yake bada mulki ga wanda yake so ba son wani mai so ba kuma kowane ne kuma shi kadai ne yake kwace mulki ga wanda ya so. Shi kadai ne ke daukaka wanda ya so kuma ya kaskantar da wanda ya so a sanda ya so kuma ko ana so ko ba a so.
In ka lura sai ka ga shi fa a halittunsa babu wanda ba ya so kuma hakikknin so to ashe in ya ba wanda kake so mulki ya jarrabe shi ne kuma in ya hana wanda kake so mulki shi ma salon jarabawa ne.
Ya ku ‘yan uwana ‘yan Nijeriya me ya fi kamata mu kama don ganin kasarmu ta inganta kuma zaman lafiya ya wadata, a gaskiya sai mun tsarkake harsunanmu daga zagin junanmu musamman ma dai shugabanninmu ko kuma gwamnatocin kasarmu in ba da wani kwakkwaran dalili ba.
Sannan ya kamata mu himmatu da yin hailala da salatin Annabi(S.A.W) da karatun Alkur’ani da sadaka da sauran ayyukan alheri don Allah Subhanahu Wata’ala ya zaba mana shugaba nagari ko kuma shugabanni masu nagarta musamman wadanda su ne suke sonmu sai su tausaya mana kuma su yi mana adalci ba wadanda mu ne muke son su ba sai su wahalshe mu kuma su wadanda suke sonmu sai su gina kasarmu ba kasashen ketare ba su ko wadanda mu ne muke son su su ba sa sonmu sai su gina kasashen ketare ba kasarmu ba.
Mu kiyayi jifan junanmu da miyagun kalamai, ballanta kuma yawo da makamai musamman a wannan rana ta yau mai dimbin tarihi a kasar na, ranar da muke gudanar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya, domi mu fa ‘ya’yan Annabi Adamu ne muna da ‘yanci mu yi zabe ne kurun amma Allah Subhanahu wata’ala shi kadai yake da hakki na yin zabe domin kuwa shi kada ne in ya zabe ka to kai ne zababbe ko wani ya zabe ka ko kar ya zabe ka to kai ne zababbe.
Ya Allah ka taimaki Nijeriya, da gwamnatocin Nijeriya da talakawan Nijeriya. Haka kuma muna rokon allah a wannan rana ta yau da muke wannan zabe ya taimake mu wajen zaben mutumin kirki.
Shawara ga shugaba nagari akwai wata kissa ta faru a zamanin Khafancin Sayyidina Ummar Bin Khaddab wadansu matasa ne sai suka zo su uku suna rike da wani balagaggen saurayi sai suka ce ya Khalifa wananne ya kasha mana mahaifinmu kuma muna so a yi masa hukuncin Allah Subhanahu Wata’ala, Khalifa ya kale shi ya tambaye shi shin kai ne ka kashe musu mahaifinsu? Dan saurayi ya ce ai ni makiyayi ne na rakuma sai wata rakumata ta shiga gonar mahaifinsu sai ta ci masa itaciya shi kuma sai ya jefe ta da wani dutse nan take sai ta mutu ni ma sai na jefe shi da wannan dutsen nan take shi ma sai ya mutu Khalifa ya ce to zan tsayar da haddin Allah a kanka, domin kai ka kashe dan’adam ne shi kuwa babansu ya kashe rakuma ne su kuma sai su biya ka rakumarka sai saurayin ya ce to ka ba ni kwana uku in je in dawo sai aka zartar da haddin Allah a kaina. Khalifa ya ce kai ! Kai da ka yi wannan aikin ya ya zan barka ka tafi ka dawo saurayi ya ce yau kwana uku da mutuwar mahaifina kuma mu biyu ne tak ‘ya’yansa daga ni sai kanwata kuma dukiyar duk da ya bari tana hannuna in an kasha ni yanzu da kanwata da dukiyar za su tagayyara amma in kuwa na je na mika mata dukiyar sai in dawo a zartar min da haddin Allah.
Khalifa ya ce to kana da wanda belinka? Saurayi sai ya nuna Abudarri ya ce wancan shi ne zai belina. Khalifa ya ce wa Abudarri kai ne za ka yi belinsa Abudarri ya ce, eh zan yi belinsa Khalifa ya ce wa Abudarri in bai dawo ba zan tsaida haddin Allah a kanka ka yarda ya ce na yarda sai saurayi ya tafi har kwana uku bai dawo ba hankalin kowa ya tashi Abudarri ya yi taushi mutane na cewa yanzu shi ke nan za a kashe Abudarri shi kuma bai ma san garin su saurayin nan ba balantana gidansu can cikin al’muru jim kadan kafin ta da ikama sai ga saurayi kwatsam a gaban Khalifa Umar, yana cewa na dawo katsai da haddin Allah a kaina.
Khalifa ya waigo cikin mamaki ya ce kai! Kai da ka samu damar guduwa ya ya aka yi kuma ka dawo sai saurayi ya ce na ji tsoro ne kada a ce a lokacina ne alkawari ya lalace tsakanin mutane kuma in har babu cika alkawari al’umma ba za ta zauna lafiyaba. khalifa ya waiga ya kalli a Abudarri ya ce kai da ba ka san shi ba kuma ba ka taba ganinsa ba, me ya sa ka lamunce shi Abudarri ya ce na ji tsoro ne kar a ce a zamanina ne taimakon wanda ba ka sani ba ya lalace kuma in mutane suka daina taimako sai ga wanda suka sani to al’umma ba za su samu zaman lafiya ba nan take sai wadanda suke bin jinin mahaifinsu suka ce ya Khalifa da ya waigo ya kalle su sai suka ce mu ma mun yafe masa.

Exit mobile version